An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

- Gwamnatin jihar Imo ta maka tsohon kwamishinan kasuwanci da masana'antu, Mbanaso a kotu

- Ana zarginsa da sata, damfarar sai da tsohon kwamishinan ya musanta aikata laifin inda ya ce sharri ake masa

- Alkalin kotun da bayar da belin tsohon ministan kuma ta dage cigaba da sauraron karar zuwa watan Satumba

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Imo ta gurfanar da tsohon kwamishinan kasuwanci da masana'antu, Best Mbanaso a kotun Majistare a jiya Litinin bisa zarginsa da aikata laifuka 11 masu alaka da zamba, sata da lalata gidajen man fetur a jihar.

Kafin afkuwar wannan lamarin, Mbanaso na hannun daman gwamna Rochas Okorocha ne amma alakarsu ta lalace a lokacin da tsohon kwamishinan ya ki goyon bayan wanda Okorocha ya ke son ya gaje shi idan ya kammala mulkinsa a jihar.

Punch ta ruwaito cewa an kama Mbanaso a ranar Laraba da ta gabata amma ya musanta aikata laifuka 11 da ake tuhumarsa da aikatawa a yayin da ya gurfana gaban alkali.

An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara
An gurfanar da tsohon kwamishina a kotu bisa zargin sata da damfara

Anyi ikirarin cewa a tsakanin 2012 zuwa 2013, Mbanaso ya karbi kayayakin ginin gidajen mai wanda kudinsa ya kai N38 miliyan daga Olison Enterprises, mallakar Cif Oliver Anopuome a lokacin da ya ke wakiltan gwamnatin jihar.

DUBA WANNAN: 2019: Dan takarar PDP ya yi tsokaci kan farin jini Buhari a arewa

An kuma ce ya karbi man fetur da diesel misalin lita 33,000 wanda kudinsu ya tasanma N5 miliyan daga Olison Enterprises.

Dan sanda mai shigar da karar, Caleb Achi, ya kuma ce tsohon kwamishinan ya rushe wata gidan mai mallakar Olison Enterprises da sunnan wai gwamnatin jihar Imo ne ta bashi umurnin aikata hakan.

Caleb ya kuma ce Mbano ya hada baki da wasu mutane sun hada baki wajen sace tankunan ajiyar man fetur na karkashin kasa da tankin ruwa duk dai mallakar Olison Enterprises.

Alkalin kotun, Adaugo Nosiri, ta koka kan yanayin da hukumar 'yan sanda ta gabatar da takardun karar. Kazalika, ta cacaki hukumar 'yan sanda saboda shigar da karar da kotun ba ta da izinin yin shari'a a kai.

Daga karshe, Alkalin kotun ta bayar da belin wanda ake tuhuma sannan ta dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Satumba a yayin da za ta jira shawarwari daga sashin gudanar da shari'a na jama'a ta jihar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel