An samu rabuwar kai tsakanin wasu manya a APC da Gwamnonin Jihohi

An samu rabuwar kai tsakanin wasu manya a APC da Gwamnonin Jihohi

Baraka na neman barkewa a Jam’iyyar APC mai mulki kamar yadda mu ka samu labari. Hakan na zuwa ne bayan wasu manya a Jam’iyyar na neman kawo sabon tsari na fitar da ‘Yan takara a 2019.

Wasu manya a Jam’iyyar APC sun samu sabani da Gwamnonin Jihohin kasar a game da tsarin tsaida ‘Yan takarar da za a ba tikitin Jam’iyya a zaben 2019. Wasu kusoshin Jam’iyyar mai mulki na nema a koma zaben kato-bayan-kato.

An samu rabuwar kai tsakanin wasu manya a APC da Gwamnonin Jihohi
Wani taro na manyan APC da aka yi kwanakin baya

Gwamnonin na APC da kuma shugabannin APC na Jihohi ba su yi na’am da tsarin zaben fitar da gwani da ake nema a kawo ba. Jiga-jigan Jam’iyyar su na so a rika yin zabe ne na kowa-da-kowa wajen fitar da wanda Jam’iyya za ta tsaida takara.

Jiga-jigan APC da ke da wannan ra’ayi na cewa duk ‘Ya ‘yan Jam’iyya za su zabi wanda ake so yayi takara a babban zabe su na ganin hakan zai fi bada damar a samu ‘Dan takarar da ya fi farin jini. Sai dai Gwamnoni ba za su yarda da wannan ba.

Jaridar The Nation ta rahoto cewa Gwamnonin APC da ke kokarin zarcewa a kan mulki su na ganin idan aka rika bada dama ayi zabe kato-bayan-kato watau kowane ‘Dan Jam’iyya ya fito ya zabi ‘Dan takarar sa, karfin su zai ragu a Jihohin su.

KU KARANTA: 2019: Bukola Saraki ya tona asirin Bola Tinubu

‘Yan Majalisun da ke Jam’iyyar APC da kuma wasu manya a Jam’iyyar su na goyon bayan wannna tsaro. Gwamnoni da Shugabannin APC na Jihohi wanda duk bakin su guda su na kukan cewa babu isasshen lokaci da za a gudanar da irin wannan zabe.

Kwanaki babban jigon Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa kato-bayan-kato za a tsaya a fitar da ‘Yan takarar APC da su rike tuta a babban zabe mai zuwa. Wasu dai a Jam'iyyar APC sam ba za su yarda da hakan ba.

Irin wannan zabe ne dai aka yi kwanan nan wajen tsaida ‘Dan takarar Gwamnan APC a Jihar Osun. Ana tunani wannan tsari zai ragewa Gwamnoni karfi tare da kuma rage kashe kudi da ake yi wajen samun tikitin Jam’iyya inji wani Sanatan Jam’iyyar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng