Jam’iyyar PDP ta zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da keta hakkin Bil Adama

Jam’iyyar PDP ta zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da keta hakkin Bil Adama

Jam’iyyar adawa ta PDP tace za tayi bakin kokarin ta wajen ganin babban Kotun Duniya watau ICC ta kama Shugaban Kasa Muhammadu Buhari saboda keta hakkin Bil Adama da cin zarafin al’umma.

Jam’iyyar PDP ta zargi Gwamnatin Shugaba Buhari da keta hakkin Bil Adama
Shugaba Buhari tare da jama'a kwanaki a babban Kotun Duniya ICC

PDP tace za tayi kira ga Jama’ar kasar nan da su tashi tsaye domin ganin an takawa yunkurin da Gwamnatin Shugaban Kasa Buhari ta ke yi na dawo da mulkin karfa-karfa na tsarin Soja a Najeriya a cikin tafiyar Damukaradiyya.

Jam’iyyar adawar tace dole ta maka Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a gaban babban Kotun ICC domin ganin an tuhumi kama-karyar da Gwamnatin sa tayi cikin shekaru 3 a kan mulki tare da kuma hukunta sa a gaban Duniya.

KU KARANTA: Wani Sanatan Najeriya yace 'Yan Sanda na neman kashe sa

Jaridar Daily Trust ta rahoto PDP tana cewa Shugaba Buhari yana kokarin maido da tsarin Soja yayin da ake tafiyar farar hula a Najeriya. Jam’iyyar tace mutanen Najeriya sun yi kokari a baya wajen watsi da tsarin mulkin Soja a Kasar.

PDP tana zargin Buhari da kokarin hana ‘Yan adawa sakat a kasar. Shugaba Buhari dai ya nuna cewa Najeriya za ta cigaba da bin dokar kasa muddin dokar ba za tayi wa dinbin rayukar al’umma barazana ba wanda hakan ya jawo suka.

Dazu kun ji cewa wani ‘Dan jarida yana neman Naira Miliyan 200 a wajen Gwamnatin Najeriya. ‘Dan jaridar yana neman Gwamnatin Buhari ta biya sa makudan kudi na keta masa hakki a gaban Kotu

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel