Babban ‘Dan Sanata Goje zai fito takarar Gwamnan Gombe a Jam’iyyar adawa

Babban ‘Dan Sanata Goje zai fito takarar Gwamnan Gombe a Jam’iyyar adawa

Mun samu labari cewa ‘daya daga cikin ‘Ya ‘yan tsohon Gwamnan Jihar Gombe watau Sanata Muhammad Danjuma Goje zai tsaya takarar Gwamna a zabe mai zuwa da za ayi a 2019.

Babban ‘Dan Sanata Goje zai fito takarar Gwamnan Gombe a Jam’iyyar adawa
Yaron Goje na nema ya canji Dankwambo a matsayin Gwamna
Asali: Depositphotos

Ahmad Goje wanda shi ne babban ‘Dan tsohon Gwamna Danjuma Goje ya shirya tsayawa takarar Gwamnan Jihar Gombe a karkashin Jam’iyyar PDP wanda ke mulkin Jihar. Goje ya yanki fam din tsayawa takara ne a farkon makon nan.

Kamar yadda mu ka samu labari daga Jaridar nan ta Daily Trust, Ahmad Goje ya bayyanawa manema labarai cewa zai yi takarar ne domin yi wa Jihar ta sa hidima. Yanzu haka dai Ahmad Goje yana cikin manya a Gwamnatin Jihar Gombe.

Ahmad Goje dai na nema ya bi sahun da Mahaifin sa ya bi amma a wata Jam’iyyar dabam. Shi Danjuma Goje yayi mulki ne daga 2003 zuwa 2011 a karkashin Jam’iyyar PDP. A 2014 ne Sanata Goje ya fice daga PDP ya koma Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: 'Dan takarar PDP Kwankwaso yayi jawabi a Jihar Shugaban Kasa

Sanata Danjuma Goje ya bar PDP ne bayan ya samu matsala da Magajin sa Ibrahim Hassan Dankwambo. Sai dai Ahmad Goje ya cigaba da aiki da Gwamnan a matsayin mai ba Gwamnan shawara kuma Darektan wani kamfani na Jihar.

Ahmad Goje yayi alkawarin marawa duk wanda PDP ta tsaida takarar Gwamna a Jihar ko da bai yi nasara ba. Bayan nan Goje yace zai yi siyasa cike da tsabta ba tare da gaba ba. Shugaban PDP a Gombe Adamu Jagafa yace za ayi adalci a zaben PDP.

Dazu kun ji labari cewa yaron Marigayi tsohon Gwamnan Kwara Ahmad Lawal zai yi takarar Gwamna a 2019 karkashin APC. Alhaji Akeem Lawal ya bayyana wannan ne a Garin Ilorin cikin 'yan kwanakin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel