Ni ba zan bada kudi domin a zabe ni ba domin na fi kowa cancanta – Ahmad Makarfi

Ni ba zan bada kudi domin a zabe ni ba domin na fi kowa cancanta – Ahmad Makarfi

Yayin da ake neman buga gangar zaben 2019, mun samu labari cewa daya daga cikin masu neman takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar adawa ta PDP ya sha alwashin doke sauran abokan takarar sa.

Ni ba zan bada kudi domin a zabe ni ba domin na fi kowa cancanta – Ahmad Makarfi
Makarfi ya fadi dalilan da ya sa yake neman PDP ta tsaida sa takara

Tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP Sanata Ahmad Muhammad Makarfi ya bayyana cewa ba ya bukatar kudi wajen samun tikitin tsayawa takarar Shugaban kasa a Jam’iyyar ta PDP. Makarfi yace ba kudi ne ke bada mulki ba.

Ahmad Makarfi wand yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa a 2019 ya bayyanawa manema labarai cewa an yi Shugabannin kasa irin su Shagari, ‘Yaradua, Obasanjo da irin su Buhari wanda ba kudi ya kawo su ba.

Tsohon Gwamnan na Kaduna ya bayyana cewa a wata Jiha da ya kai ziyara, an bayyana masa cewa sauran masu neman takarar su na raba kudi. Makarfi yace ba zai bada ko sisi ba domin kuwa shi ya cancanta da mulkin kasar.

KU KARANTA: Buhari da Shugaban APC ba za su iya ceton wani Sanatan APC ba

Sanata Makarfi dai yana sa rai kokarin da yayi wa Jam’iyyar a lokacin yana rikon kwarya ya ba sa damar samun tikitin PDP a zaben Shugaban kasa. Makarfi yace PDP ta kama hanyar mutuwa amma ya farfado da ita a baya.

A lokacin da Makarfi yake bayani ga ‘Yan jarida a Legas jiya yace bai taba sauya-sheka ba, kuma ya rike shugabancin PDP, sannan kuma yana cikin manya a Majalisar Dattawa har na shekaru 8 don haka ya fi kowa cancanta a PDP.

Dazu ne kuma ku ka ji cewa Atiku Abubakar ya jadaddawa sauran ‘Yan takarar PDP sai ya ga abin da ya turewa buzu nadi a zaben da za ayi. Atiku yace shi ya dace ya rike mulkin Kasar nan a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel