‘Yan siyasar da za su yi takarar Gwamna a Jihar Kwara a zaben 2019

‘Yan siyasar da za su yi takarar Gwamna a Jihar Kwara a zaben 2019

Mun kawo maku jerin ‘Yan siyasar da ake tunani za su tsaya takarar Gwamna a Jihar Kwara. Jihar dai ce Mahaifar Shugaban Majalisar Datawa Bukola Saraki inda yayi Gwamna tun 2003 har 2011 a karkashin PDP har ta kai ya zama Sanata.

‘Yan siyasar da za su yi takarar Gwamna a Jihar Kwara a zaben 2019
Tsohon Ministan PDP zai nemi takarar Gwamnan Kwara a 2019

Daga cikin masu neman kujerar Gwamnan akwai wani Abokin siyasar Bukola Saraki a PDP da kuma Yaron tsohon Marigayi tsohon ‘Dan adawar sa. Ana tunani kuma wani Ministan Buhari ya shiga cikin sahun masu takarar.

1. Bolaji Abdullahi

Tsohon Minista a lokacin Jonathan kuma tsohon Sakataren yada labarai na APC watau Bolaji Abdullahi yace zai jarabba neman takarar Gwamna a Jihar ta Kwara. Bolaji yana cikin wadanda su ka bar APC tare da Bukola Saraki.

KU KARANTA: Buhari ya lissafo ayyukan da yayi a Jihar Bukola Saraki

2. Akeem Lawal

Labari ya zo mana cewa Yaron Marigayi tsohon Gwamnan Kwara Ahmad Lawal zai yi takarar Gwamna a 2019 karkashin APC. Alhaji Akeem Lawal ya bayyana wannan ne a Garin Ilorin. Saraki ne dai ya tika Mahaifin sa da kasa a 2003.

3. Lai Mohammed

Ministan yada labarai Lai Mohammed yana cikin wadanda su kayi takara da Saraki a 2003. Sai Lai ya fara nuna cewa ba zai nemi Gwamna a Kwara ba a zaben badi na 2019. Ministan kasar dai ya dade da wannan buri a ran sa.

Kwanan nan ne Gwamnatin Najeriya yayi kaca-kaca Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki inda tace bai taba marawa tafiyar Shugaba Buhari baya ba ko da yake Jam’iyyar APC mai mulki.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel