Dalilin da yasa ba zan alanta niyyar takarana a Kano ba - Kwankwaso

Dalilin da yasa ba zan alanta niyyar takarana a Kano ba - Kwankwaso

- Sanata Rabiu Kwankwaso zai tsaya takarar shugaban kasa karkashin PDP

- Zai alanta niyyar takararsa ranan Laraba

- Har yanzu ba'a samu yin sulhu tsakaninsa da tsohon abokinsa ba

Tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya bayyana dalilin da ya sa ba zai alanta niyyar takaran shugaban kasa karkarshin jam’iyyar PDP a jihar Kano ba. Ya zabi Abuja domin yin hakan.

Sanata Kwankwaso wanda suke takun saka da gwamnan jihar, wanda tsohon abokin siyasarsa ne, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa zai alanta niyyar takararsa ranan Laraba, 29 ga watan Agusta a birnin tarayya Abuja.

KU KARANTA: Kalolin Kiswa 7 da akayi amfani da su tun zamanin manzon Allahﷺ (Hotuna)

Mun samu wannan rahoto ne a jawabin da mai magana da yawun Kwankwaso, Binta Sipikin, tayi a hiran da tayi a jaridar Premium Times yau Litinin. Sipikin ta ce Abuja birnin tarayya ce kuma abokan siyasa da masoya Kwankwaso daga fadin tarayya za su halarci taron, dalilin da yasa aka zabi Abuja kenan.

Ta kara da cewa ba taron yan jihar Kano bane, kuma zai fi sauki ga mutane su daga fadin tarayya.

Tace: “Zai alanta Abuja saboda birnin tarayya ce, wannan taron kasa ce. Zaben Abuja zai fi sauki ga mutanen da za su zo daga sassan kasa daban-daban.”

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayyana cewa Kwankwaso ba zai isa gudanar da wannan taro a jihar Kano ba.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel