Musulmi Miliyan 57.7 ne sukayi aikin Hajji a cikin shekaru 24

Musulmi Miliyan 57.7 ne sukayi aikin Hajji a cikin shekaru 24

- Musulimi Miliyan 52,683,893 suka gudanar da aikin Hajji daga shekara ta 1995 (1416H) zuwa 2016 (1437H)

- Daga shekara ta 2017 zuwa 2018 an samu karuwar mahajjata 19,553

- Shekara ta 2012 ta fi kowace shekara yawan adadin Mahajjata, yayin da aka samu mafi karancin mahajjata a shekara ta 1998

Rahotanni da bayanan da Hukumar kididdiga ta kasar Saudiya ta tattara kuma ta fitar ya bayyana cewa Musulumi Miliyan 52,683,893 ne suka gudanar da aikin Hajji a cikin shekaru 24.

A wani rahoto da hukumar ta fitar, ya nuna cewa mutane Miliyan 2,371,675 da suka hada da maza Miliyan 1,327,127 da mata Miliyan 1,044,548 ne suka gudanar da aikin Hajjin wannan shekartar ta 2018.

Jadawalin kididdigar wanda ya fara daga shekara ta 1995 (1416H) zuwa 2016 (1437H), ya nuna cewa Musulmi maza da suka fito daga yankin kasashen labarawa Miliyan 16,027,649 ne suka gabatar da aikin hajji yayin da maza daga sauran kasashe, Miliyan 31,932,447 ne suka yi aikin hajjin, wanda ya hada maza Miliyan 47,960,096 a cikin shekaru 22.

KARANTA WANNAN: Fasinjoji na mutuwa saboda direbobi masu matsalar gani -FRSC

Kididdigar shekara ta 2017 wacce ta nuna adadin mutane Miliyan 2,352,122 da sukayi aikin Hajji, ta bayyana adadin maza Miliyan 1.33 da mata 1.02 ne suka gabatar da aikin hajji a wannan shekar.

Adadin Musulmin da sukayi aikin Hajji a cikin shekaru 24 daga shekara ta 1995 (1416AH) zuwa 2018 (1439AH) ya tsaya a Miliyan 52,683,893 maza da mata.

Banbancin da ke tsakanin shekaru biyu da suka gabata ya nuna cewa an samu karuwar mahajjatan da mutane 19,553 a shekara ta 2018, adadin da ya haura na shekara ta 2017

An samu wadannan rahotanni ne ta hanyar musayar sakwanni ta kafar Email da kuma shafin yanar gizo na hukumar.

Sai dai an samu mafi yawan adadin mahajja a shekara ta 2012 inda ‘yan yankin Saudiya mutane Miliyan 1,408,641 ne suka yi aikin hajjin, yayin da mutane Miliyan 1,752,932 daga wasu kasashen suka gudanar da aikin hajjinsu a wannan shekarar, wanda ya bada adadin mahajjata 3,161,573.

A yayin da yawan adadin mahajjatan na shekara ta 2012 ya fi adadin kowace shekara, a hannu daya kuma, adadin mahajjatan shekara ta 1998 ne ya fi kowanne yin kasa, inda aka samu mahajjata 1,831,998 da suka hada da mahajjata 775,268 da suka fito daga yankin saudiya da kuma mutane Miliyan 1,056,730 da suka fito daga wasu kasashe.

Dangane da mahajjatan Nigeria kuwa, a farko an amince wa mahajjata 92,000 ne kawai, har sai a shekara ta 2013 in da aka rage yawan mahajjatan zuwa 76,000, kafin daga bisani kuma aka mayar da shi 95,000.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel