Mai ba Jonathan shawara ya fadawa Kwankwaso cewa gaba ta fi baya yawa

Mai ba Jonathan shawara ya fadawa Kwankwaso cewa gaba ta fi baya yawa

Mun samu labari cewa wani tsohon Hadimin Goodluck Jonathan ya soki Sanatan Kano Rabiu Musa Kwankwaso. Hakan na zuwa ne bayan tsohon Gwamnan ya ziyarci tsohon Shugaban kasar kwanaki.

Mai ba Jonathan shawara ya fadawa Kwankwaso cewa gaba ta fi baya yawa
Omokri ya tado abin da ya faru tsakanin Jonathan da Kwankwaso a baya

Reno Omokri wanda shi ne mai ba Goodluck Jonathan shawara a kafofin sadarwa na zamani lokacin yana Shugaban kasa ya tunawa Rabiu Musa Kwankwaso abin da ya faru kafin zaben 2015 lokacin da Sanatan yana Gwamnan Kano.

Sanata Rabiu Kwankwaso yayi ta sukar Goodluck Jonathan lokacin yana mulki, daga karshe dai Gwamnan ya fice ya bar PDP. Yanzu dai babban ‘Dan siyasar yana neman goyon bayan Jonathan a shirin neman takarar da yake yi a PDP.

KU KARANTA: Kwankwaso zai kaddamar da shirin takara a karkashin PDP

Reno Omokri yayi amfani da shafin sa na Tuwita inda ya gargadi Sanatan na Kano ta tsakiya da wanin sa ma cewa su bi a hankali da rayuwar siyasa domin kuwa wanda ka share a yau, shi za ka nemi ya daga ka sama a wani lokacin kamar yadda aka yi.

Akwai dai lokacin da Jonathan da mukarraban sa su kayi amfani da tsinstiya su ka share wurin da Goodluck Jonathan ya ziyarta domin nuna tsantsar adawa. Duk da wannan kuma kwatsam sai aka ga Kwankwaso tare da Jonathan kwanaki har gida.

Kwankwaso ya gana da Jonathan har gidan sa kwanan nan inda bayan na tsohon Gwamnan ya fito shafin sa na Tuwita jiya ya bayyana cewa idan dai ma ana maganar shugabannin da su kayi wa Kasar nan hidima to dole a kira irin su Jonathan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel