Kwankwaso zai kaddamar da shirin tsayawa takarar Shugaban kasa

Kwankwaso zai kaddamar da shirin tsayawa takarar Shugaban kasa

Labari ya iso mana ba da dadewa ba cewa tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sa ranar tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP.

Kwankwaso zai kaddamar da shirin tsayawa takarar Shugaban kasa
Kwankwaso zai yi takarar Shugaban kasa a 2019

Tsohon Gwamnan na Jihar Kano Rabiu Musa Kwankwaso zai kaddamar da shirin sa na tsayawa takarar fitar da gwani na Shugaban Kasar Najeriya a makon nan. Kwankwaso na sa ran samun tikitin Jam'iyyar PDP a zaben fitar da gwani da za ayi.

A Ranar Laraba 29 ga Watan Agustan nan ne Sanatan Kano ta tsakiya zai shirya taron tabbatar da tsayawa takarar Shugaban kasa a zaben da za ayi shekara mai zuwa. Za ayi wannan gangamin ne a babban Birnin Tarayyar Najeriya.

KU KARANTA: Wani tsohon Gwamnan PDP ya koma APC a Kudancin Najeriya

Kamar yadda mu ka samu labari, za ayi taron ne a filin taro na Eagles Square da kimanin karfe 10:00 na safe. Ana tunani jama’a da dama musamman Magoya bayan babban ‘Dan siyasar za su cika Garin Abuja domin wannan taro na musamman.

Kawo yanzu dai tsohon Gwamnan yana cigaba da ganawa da manyan PDP na Kasar daga ciki har da tsofaffin Shugaban kasa irin su Goodluck Jonathan. A makon jiya kuma Kwankwaso ya gana wani jigo a PDP Tsohon Gwamna James Ibori.

Dazu kun ji labari cewa Rabiu Kwankwaso ya kai wa Gwamnan Taraba Darius Ishaku ziyara a Abuja yayin da yake cigaba da shirin neman tsayawa takara a zaben na 2019. Shugaban na ‘Darikar Kwankwasiyya zai nemi doke Buhari a 2019.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel