Dalilin da yasa nayi tafiyar kafa mai tsawo ranar Sallah - Buhari

Dalilin da yasa nayi tafiyar kafa mai tsawo ranar Sallah - Buhari

A ranar da aka yi babba Sallah ne shugaba Buhari ya yi tafiyar kafa mai tsawon mita 800 zuwa gidansa baya idar da Sallar idi. Lamarin tafiyar kafar da shugaba Buhari ya yi ta jawo cece-kuce da tofa albarkacin baki a tsakanin 'yan Najeriya.

Yayin da wasu ke ganin shugaba Buhari yayi wannan tafiya ne domin gwada farin jininsa wasu kuwa cewa suke ya yi tafiyar ne domin nuna cewar yanzu fa garau yake, lafiya ta samu.

Ko a ranar da shugaba Buhari ya yi doguwar tafiyar ta kafa sai da mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Malam Garba Shehu, ya bayyana cewar yanzu batun kokwanto a kan koshin lafiyar shugaba Buhari ya zama tsohon zance tunda duk duniya kowa ya ga yadda ya taka a kafa daga masallacin idi zuwa gidansa a garin Daura.

Dalilin da yasa nayi tafiyar kafa mai tsawo ranar Sallah - Buhari
Dalilin da yasa nayi tafiyar kafa mai tsawo ranar Sallah - Buhari

DUBA WANNAN: Riba da amfanin da ke cikin soyaya ko auren mace soja

Sai dai da yake bayyana dalilin da ya saka shi yin wannan doguwar tafiyar kafa, shugaba Buhari ya bayyana cewar yayi hakan ne domin bawa jama'a damar ganinsa kasancewar motar da yake ciki a rufe take da bakin gilashi.

"Ni banyi tattaki domin tabbatar wa da kowa cewar ina da koshin lafiya bane, na zabi yin tafiyar kafa ne domin bawa jama'a damar gani na kasancewar motar da nake ciki a rufe take da bakin gilashi," in ji shugaba Buhari.

Wannan kalamin na shugaba Buhari ya ci karo da abinda da mai taimaka masa, Malam Garba Shehu, dake nuna tamkar shugaba Buhari ya yi tattakin ne domin musanta masu cewar bashi da koshin lafiya da zai cigaba da zama shugaban kasar Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel