Jam'iyyar APC za ta yi nasara a Zaben 2019 - Buhari ya yi bugun Gaba

Jam'iyyar APC za ta yi nasara a Zaben 2019 - Buhari ya yi bugun Gaba

A ranar Juma'ar da ta gabat ne shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi bugun gaba tare da cika baki da cewa, jam'iyyar APC za ta yi lashe babban zabe na 2019.

Wannan bugun gaba na shugaba Buhari wani martani ne ga shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki, wanda a kwana-kwanan nan ya bayyana cewa jam'iyyar adawa ta PDP ce za ta lashe zaben 2019 mai gabatowa.

Shugaba Buhari yake cewa, ko shakka ba bu duk wadanda suka gaza wajen fahimtar hakan tare da ra'ayin rashin nasarar da jam'iyyar sa ta APC za ta yi sun hau wani doki ne na talala da ba bu inda za ya kai su.

Jam'iyyar APC za ta yi nasara a Zaben 2019 - Buhari ya yi bugun Gaba
Jam'iyyar APC za ta yi nasara a Zaben 2019 - Buhari ya yi bugun Gaba

A ranar Larabar makon da ya gabata ne Saraki ya shaidawa mambobin jam'iyyar sa ta PDP reshen jihar Kwara cewa, nasarar zaben 2019 ta na ga jam'iyyar reshen jihar da kuma kasa baki daya.

Sai dai cikin wata sanarwa da sa hannun kakakin shugaban kasa, Mallam Garba Shehu, shugaba Buhari ya bayyana cewa, nasarar da jam'iyyar APC ta yi a zabukan maye maye gurbi cikin jihohin Bauchi, Katsina da kuma Kogi shaida ce dake haskaka nasarar da jam'iyyar za ta yi a zaben 2019.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Shugaba Buhari ya karbi baƙuncin wasu 'Kungiyoyi a garin Daura

Legit.ng ta fahimci cewa, shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin karbar bakuncin wakilan shugabannin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina a mahaifar sa ta garin Daura.

A yayin da shugaba Buhari ke ci gaba da hutun sa na bikin babbar Sallah, yana kuma ci gaba da karbar bakuncin kungiyoyi daban-daban inda suke ziyartar sa domin taya murna ta bikin wannan lokaci.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://business.facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel