An damke mata biyu cikin 'yan bindigan da suka addabi Zamfara

An damke mata biyu cikin 'yan bindigan da suka addabi Zamfara

Jami'an sojin Najeriya na hadin gwiwa ta Operation Sharan Daji da ke yakar 'yan bindiga a jihar Zamfara sunyi nasarar damke wasu 'yan bindiga mata guda biyu tare da wasu 'yan bindiga 50 a jihar.

Wannan sanarwan ta fito ne daga bakin Direktan yada labarai na hedkwatan tsaro, Brig. Janar John Agim yayin da ya kira taron manema labarai a jiya Juma'a a garin Gusau don sanar da su nasarorin da rundunar Sharan Dajin ke samu.

Ya ce a halin yanzu, rundunar tayi nasarar kashe rikakun 'yan bindiga da masu aikata laifi da suke adabar jama'a cikinsu har da Danboko da Danbuzuwa.

Am damke mata biyu cikin 'yan bindigan da suka addabi Zamfara
Am damke mata biyu cikin 'yan bindigan da suka addabi Zamfara

Janar Agim ya kuma yaba da kokarin mayakan sojin saman Najeriya da suka bayar da gudunmawa wajen yin luguden wuta a mabuyar 'yan bindigan da ke dajin Sububu da Rugu.

DUBA WANNAN: Hukumar 'yan sanda ta gayyaci Fani Kayode saboda kalaman kin addini

Ya kuma kara da cewa sojin sunyi nasarar damke dilalan makamai biyu da kuma 'yan bindiga mata guda biyu.

Agim ya ce an kwato muggan makamai sama da 20 tare da wasu makamai masu hatsari da aka kera a Najeriya.

"Sauran abubuwan da aka kwato sun hada da babura 38, wayoyin salula sama da 30 da wasu mutane uku da 'yan bindigan su kayi garkuwa dasu tare da kudi N500,000 daga hannun masu garkuwa da mutanen," inji Agim.

Ya ce sintirin da jami'an sojin ke yi a kauyuka da kasuwanni da sauran wurare ya bawa jama'a kwarin gwiwar cigaba da lamuransu na yau da kullum ba tare da fargaban 'yan bindigan za su sake far musu ba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel