A kwana a tashi: Gwamnonin Arewa guda 3 da suka yi karakaina da Iyayen gidansu a zabukan 2019

A kwana a tashi: Gwamnonin Arewa guda 3 da suka yi karakaina da Iyayen gidansu a zabukan 2019

Zaben 2019 zabe da zai zo da sarkakiya da dama, wanda masana suka bayyana shi a matsayin wani zakarar gwajin dafi ne, musamman a jihohin da gwamnoninsu zasu kammala wa’adin mulki amma suna hangen kujerar Sanatan da iyayen gidansu suke kai, wanda hakan zai hada su rikici da iyayen gidansu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito daga cikin jihohin nan akwai jihar Zamfara, inda za’a gwada kwanji tsakanin Sanata Ahmed Sani Yariman Bakura da yaronsa Gwamna Abdul Aziz Yari, sai kuma Yobe inda Gwamna Ibrahim Gaidam yake hangen kujerar Sanata Bukar Abba, da kuma Borno, tsakanin Gwamna Kashim da Sanata Ali Modu Sheriff.

KU KARANTA: Yadda wasu yan bindiga dadi guda 2 suka gamu da ajalinsu a jihar Kaduna

Zamfara:

Alamu da kuma hasashe irin na masana siyasar jihar Zamfara sun bayyana cewa gwamnan jihar Abdul Aziz Yari na da burin tsayawa takarar waklin al’ummar Zamfara ta yamma a majalisar dattawa, kamar yadda majiyar Legit.ng ta ruwaito.

Sai dai tsohon gwamnan jihar Ahmed Sani Yariman Bakura ne yayi dare dare akan wannan kujera tun shekarar 2007, don haka matukar batun takarar Yari ta tabbata, tabbas alakarsa da maigidansa zata lalace.

Yobe:

Maganar da ake yi a yanzu shine gwamnan jihar Yobe, Ibrahim Gaidam wanda yana daga cikin gwamnonin da suka fi dadewa a kujera ya kammala wa’adinsa na shekaru goma, kuma ya tabbatar da aniyarsa ta tsayawa takarar Sanatan Yobe ta gabas.

Sai dai kalubalen da yake fuskanta shine maigidansa, kuma tsohon gwamnan jihar Bukar Abba Ibrahim ne yake kan wannan kujera, a kwanakin baya ma an jiyo shi yana cewa zai cigaba da zama Sanata har sai ya mutu, don haka babban kalubale ne a gaban Gaidam

Borno

Akwai fargabar ruwa zata yi tsami tsakanin gwamnan jihar Kashim Shettima da Sanatan Borno ta tsakiya, Sanata Kaka Bashir Garbai idan har gwamnan ya yanke shawarar tsaya takarar kujerar, musamman yadda tun yanzu yan siyasa sun fara yin kiraye kiraye a gareshi.

Wani abu dake sanya jama’a ganin Shettima zai tsaya duk da cewa bai fada shine ganin yadda ba’a ganin fastocin Sanata Kaka a gari, kuma ba’a ji shi yana fadin zai sake tsayawa ba, bugu da kari wasu jama’a na ganin baya wakiltarsu yadda ya kamata.

Amma kuma akwai wasu rahotannin dake cew Shettima yace ba zai tsaya takarar komai ba, cewa zai koma gidane kawa ya huta, ya cigaba da harkokin kasuwancinsa da noma, amma duk da haka fastoncinsa na neman takara sun cika garin Maiduguri.

Babban rikicinma shine idan tsohon gwamnan jihar, kuma maigidan Gwamna Shettima, Ali Modu Sheriff ya yanke shawarar komawa majalisar dattawa kamar yadda ake yada jita jita, idan har hakan ya tabbata, takarar zata yi zafi, kuma APC zata rabiu.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel