Ambaliyar ruwa ta mamaye kananan hukumomi uku a jihar Kaduna

Ambaliyar ruwa ta mamaye kananan hukumomi uku a jihar Kaduna

Cikin 'yan kwanakin nan hukumar kula da muhali na jihar Kaduna (KEPA) ta yi gargadin cewa akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wasu sassan jihar inda ta gargadi wasu mutane da ke zaune a wasu unguwani su tashi daga gidajensu.

Ambaliyar ruwa ta mamaye gidajen mutane da dama a kananan hukumomi uku na jihar Kaduna sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya da aka kwarara a daren ranar Alhamis.

Sakataren hukumar agaji na jihar (SEMA), Mr Ben Kurah ne ya bayyana hakan a yayin da ya kai ziyarar gani da ido a wuraren da lamarin ya shafa, ya kuma kara da cewa ba'a rasa rayyuka ba sakamakon ambaliyar.

Ya ce toshewar magudanun ruwa da kuma yin gine-gine a hanyar ruwa ne ya janyo afkuwar ambaliyar ruwan.

Ambaliyar ruwa ta mamaye kananan hukumomi uku a Kaduna
Ambaliyar ruwa ta mamaye kananan hukumomi uku a Kaduna

A cewarsa, nauyin bibiyan wuraren da ambaliyar ya shafa da kiyasta irin asarar da akayi nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar.

DUBA WANNAN: Shugaba Buhari yana gudanar da manyan ayyuka a Kudu - Tsohon gwamna Kalu

Ya ce wuraren da ambaliyar ruwar ya shafa sun hada da Kigo road a Arewacin Kaduna; Barnawa a Kudancin Kaduna, Narayi da Sabon Tasha a karamar hukumar Chikun da sauran wurare.

Ya ce a kalla mutane 30 sun rasa matsiguninsu a unguwar Romi kuma a halin yanzu suna zaune ne a makarantar faramare a unguwar.

"Za mu yi hadin gwiwa tare da sauran masu ruwa da tsaki don ganin cewa an kula da dukkan wadanda lamarin ya shafa," inji Kurah.

Ya kuma sake kira ga jama'ar jihar su cigaba da sanya idanu tare da tsaftace magudanun ruwa saboda har yanzu damina ba ta wuce ba.

Manema labarai sun ruwaito cewa ambaliyar ruwan ta afku ne sakamakon ruwan sama mai yawa da aka fara tun daren Alhamis har zuwa safiyar Juma'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel