Sultan ya cika 62: Shugaban Majalisar Tarayya yayi wa Sarkin Musulmi addu’ar tsawon kwana

Sultan ya cika 62: Shugaban Majalisar Tarayya yayi wa Sarkin Musulmi addu’ar tsawon kwana

Labari ya kai gare mu cewa Shugaban Majalisar Wakilai ta Tarayya Rt. Hon. Yakubu Dogara ya taya Mai martaba Sarkin Musulmi Alhaji Saad Abubakar III murnar cika shekaru 62 a Duniya a wata takarda.

Sultan ya cika 62: Shugaban Majalisar Tarayya yayi wa Sarkin Musulmi addu’ar tsawon kwana
Shugaban Majalisa ya aikawa Sarkin Musulmi sako

Yakubu Dogara ya jinjinawa Sultan inda ya yabe sa a matsayin shugaban kawo zaman lafiya da kuma wanzar da adalci a Najeriya. Dogara ya kuma yabawa Sarkin Musulmi wajen kokarin da yake yi na hada kan daukacin al’umma.

Shugaban Majalisar Wakilan Kasar yace Mai martaba Sa’ad Abubakar III ba ya nuna bambancin addini da kabila wajen tafiyar da sha’anin sa. Yakubu Dogara yace shakka babu Mai martaban ya cika abin koyi a fadin Najeriya gaba daya.

KU KARANTA: Masu sauya sheka ba su gaba na - Inji Buhari

A takardar da Yakubi Dogara ya aikowa Sarkin Musulmin kasar, yayi addu’a Ubangiji ya kara masa lafiya da basira a kan kujerar sarauta. Dogara ya bi sahun daukacin al’umma da su ka taya Sarkin Musulmin murnar cika shekara 62.

Kwanaki Tsohon Dogarin Shugaban kasa Muhammadu Buhari a lokacin mulkin Soja Mustapha Jokolo ya soki manyan shugabannin Arewa har da Sarkin Musulmi na yin shiru game da matsalolin da Arewa ta ke fuskanta a Gwamnatin nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel