Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da yayi ma talaka aiki kamar Buhari

Babu wani shugaban kasa a tarihin Najeriya da yayi ma talaka aiki kamar Buhari

Fitaccen lauya mai mukamin SAN, kuma Kaakakin yakin neman zaben shugaban kasa Muhammadu Buhari, Festus Keyamo, ya bayyana cewa tun da aka dawo Dimukradiyya a shekarar 199 ba’a taba yin shugaban daya taimaka talaka ba kamar shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Legit.ng ta ruwaito Keyamo ya bayyana haka ne a yayin kaddamar da kumgiyar yakin neman zaben Buhari da Osinbajo a garin Ilori, inda yace babu wata gwamnati data kwato kudaden sata kamar gwamnatin shugaba Buhari.

KU KARANTA: Kungiyar kwadago ta fatattaki ma’aikata daga ofisoshinsu don a fara yajin aiki sai baba ta ji

“Gwamnatin data shude bata da kishin talaka ko kadan, bata tausayin talaka, tsarin data samar ba tsarin tallafa ma talakawa bane, kuma idan kuka duba kudaden da aka samu a shekaru 16 da suka gabata da abinda aka yi dasu, ka hada da ayyukan da Buhari yayi, zaka gane haka.

“A shekaru 16 da suka yi a mulki basu yi wani aiki a yankin kudu masu gabas ba daya wuce gina hanyar Onitsha zuwa Owerri, amma a shekaru uku kacal Buhari yana gina manyan hanyoyi guda hudu, idan Buhari zai yi ma talaka yaki, me yasa talaka ba zai yi masa yaki ba?” Inji shi.

Daga cikin ayyukan da suka shafi talaka da Buhari yayi wanda Keyamo ya zayyano sun hada da biyan tsofaffi da gajiyayyu naira dubu biyar biyar, ciyar da daliban firamari miliyan takwas, bayar da bashi mai saukin kudin ruwa na naira dubu dari biyu da hamsin ga kananan yan kasuwa.

Daga karshe Keyamo yayi kira ga Talakawa dasu tabbata sun zabi Buhari a 2019, sakamakon kafin zuwansa jihohi 24 basa iya biyan albashi, amma daga zuwan Buhari ya kawar da wannan matsalar.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng