Dandalin Kannywood: Jaruma Rukayya Dawayya ta yi kaca-kaca da wata sabuwar jaruma

Dandalin Kannywood: Jaruma Rukayya Dawayya ta yi kaca-kaca da wata sabuwar jaruma

- Dawayya ta yi kaca-kaca da wata sabuwar 'yar fim

- Tace karya take tace bata san taba

- Auren ta bai dade da mutuwa ba

Daya daga cikin fitattun tsaffin fuskokin masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood mai suna Rukayya Umar Santa da aka fi sani da Rukayya Dawayya ta nuna rashin jin dadin ta game da wata sabuwar jarumar fim din da ta nuna bata san ta ba.

Dandalin Kannywood: Jaruma Rukayya Dawayya ta yi kaca-kaca da wata sabuwar jaruma
Dandalin Kannywood: Jaruma Rukayya Dawayya ta yi kaca-kaca da wata sabuwar jaruma

KU KARANTA: Wata uwa ta auri dan ta ta kuma bada dalili

Rukayya Dawayya wadda a yan kwanakin da suka gabata ne muka kawo maku labarin fitowar ta daga gidan mijin ta ta bayyana rashin jin dadin nata ne a shafin ta na dandalin sada zumunta na Instagram.

Legit.ng ta samu cewa duk da yake dai bata kama suna ba, amma dai da alama sabuwar jarumar ta bata mata rai sosai inda har hakan ya ja ta tunzura ta ta kuma huce haushin ta a dandalin sada zumuntar.

Ga dai abun da ta fada nan:

"Bude idonki sosai ki ganni. karyane kice kina masana antar kannywood baki sanni bah. kokice bakisan sunana bah wlh karya kike. daga 10 years zuwa yanzu duk wacce ta shigo industry mutagani tashigo. idan kinzo da Alkhairi kiga Alkhairi idan kinshigo da sharri ko kwadayi duk kigani a kwaryar shanki. karyar banza. sorry my fan's wata banzace tabani haushi."

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel