'Yan sanda sun dakile wani yunkurin kona coci a jihar arewa

'Yan sanda sun dakile wani yunkurin kona coci a jihar arewa

Hukumar 'yan sanda ta karyata rahotannin dake cewa wasu matasa sun kona coci a garin Jos. Hukumar ta ce anyi yunkurin kona cocin Katolika amma jami'anta sunyi gagawar dakile yunkurin.

Hukumar 'yan sanda reshen jihar Plateau sun sanar da cewa sun dakile yunkurin da wasu matasa su kayi na kona wani Cocin katolika da Kongo Rosha dake karamar hukumar Jos ta Arewa na jihar.

Jami'in hulda da jama'a na 'yan sandan jihar, Terna Tyopev ya shaidawa Premium Times cewa lamarin ya afku ne a ranar Laraba misalin karfe 10.20 a dare.

'Yan sanda sun dakile wani yunkurin kona coci a jihar arewa
'Yan sanda sun dakile wani yunkurin kona coci a jihar arewa

Ya ce, "ba gaskiya bane rahotannin da wasu kafafen yada labarai ke yadawa na cewa an kona cocin. Ba'a kona cocin ba. Anyi yunkurin konawa amma 'yan sanda sun dakile yunkurin bayan DPO na yakin, Musa Hasan, ya sanar da jami'an hukumar."

DUBA WANNAN: Sabuwar rikici ta barke a jam'iyyar PDP a wata jihar Arewa

Mr Tyopve ya ce, "An kira waya misalin karfe 10.30 na dare inda aka sanar da rundunar 'yan sandan cewa wasu matasa na barazanar kona Cocon Katolika da ke Kongo Rosha.

"Bayan an kira mu a waya, mun tatara jami'an mu muka garzaya inda abin ke faruwa. Da isar mu sai muka gano cewa bangarori biyu ne ke rikici saboda wata budurwa mai suna Moren tayi kai karar cewa wasu matasa sunci zarafinta. Wadanda ta kaiwa kara kuma suka taso don su gwabza da dayan bangaren.

"Bayan sun hadu, rikicin ya barke ne bayan wani an raunata wani matashi mai suna Ayuba Damina, daga bayan an garzaya dashi zuwa Asbitin Ola don yi masa magani," inji shi.

Mr Tyopev ya ce a halin yanzu zaman lafiya ya samu kuma mutane suna cigaba da harkokinsu kamar yadda suka saba.

Ya kuma ce DPO na yankin ya kira taro da iyayen matasan saboda su gargadi yaransu. Kazalika, an fara gudanar da bincike domin gano wadanda suke da hannu cikin lamarin domin a hukunta su.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel