Kada ku bari 'yan siyasa su yi amfani da ku - Sarkin Musulmi ga matasa

Kada ku bari 'yan siyasa su yi amfani da ku - Sarkin Musulmi ga matasa

- Sarkin Musulmi ya ja kunnen matasa akan ‘yan siyasar kasar

- Ya ce kada su bari suna amfani da su wajen aikata barna

- Hakan na kunshe ne a sakonsa na babban Sallah

Mai martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Abubakar Sa’ad ya shawarci matasa da kada su bari 'yan siyasa su yi amfani da su, a lokacin siyasa suna saran junan su, suna shaye shaye alhali 'ya'yansu siyasar ba su gun.

Sarkin ya bayyana hakan ne a jawabin da yake gabatarwa a fadar sa na bikin sallah babba.

Kada ku bari 'yan siyasa su yi amfani da ku - Sarkin Musulmi ga matasa
Kada ku bari 'yan siyasa su yi amfani da ku - Sarkin Musulmi ga matasa

Ya ce "Idan kuna son Buhari, hanyar da za ku tabbatar da nasarar sa ita ce ku karbi katin zabenku, haka shi ma Gwamna Tambuwal da sauran 'Yan takarar".

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Sojoji sun kai mamaya Ikorodu a kokarinsu na gano yan kungiyar asirin da suka kashe wani soja

Ya kara da cewa "Mu rika yin siyasa kamar yadda ya kamata, mu kaucewa kalaman batanci da rarrabuwar kawuna a cikin siyasa. Sannan kuma bayan zabe duk wanda Allah Ya baiwa nasara mu bashi goyon baya domin ya samu nasara".

A baya Legit.ng ta rahoto cewa kungiyoyin fafutuka a jihar Nasarawa sun nuna damuwarsu kan yawaitar mambobin kungiyar Hakika a jihar da kuma yadda matasa ke shiga kungiyar.

Wani masanin harkar tsaro, Dakta Nwani Aboko, ya laburta wannan abu ne a taron da kungiyar North East Regional Initiative (NERI) ta shirya kan dakile tsatsauran ra’ayi a garin Lafiya, babban birnin jihar Nasarawa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng