An rufe babbar gadar Lagas

An rufe babbar gadar Lagas

Gwamnatin jihar Lagas ta ce za ta rufe babbar gadar nan mai muhimmanci da ta hada tsibirin Lagas da sauran unguwannin birnin domin binciken ko gadar na bukatar gyara.

Gadar wadda ake kira third Mainaland Bridge za a rufe ta ne na tsawon kwana hudu kamar yadda gwamnati ta yi alkawali.

Kwamishinan ayyuka na jihar Ade Akinsanya ya ce an tanadi jami'an kula da zirga-zirga a sauran hanyoyi domin saukaka wa cunkoso a birnin.

Gadar mai tsawon kusan kilomita 12 an kaddamar da ita ne a shekarar 1990, lokacin mulkin tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Basamasi Babangida.

An rufe babbar gadar Lagas
An rufe babbar gadar Lagas

Ana kallon gadar a matsayin mai matukar muhimmanci a jihar wacce akewa lakabi da cibiyar kasuwancin Najeriya.

KU KARANTA KUMA: Muna bukatar Buhari ya sake kera tattalin aziki – Tinubu

Matakin dai zai haifar da cushewar motoci a sauran hanyoyin da ma'aikata da 'yan kasuwa za su bi domin isa cikin birnin jihar.

Cushewar hanyoyin kuma zai fi shafi ma'aikata da 'yan kasuwa musamman lura da gadar ita hanya mafi sauki ta shiga birnin.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng