Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel

Mamba mai wakiltar karamar hukumar Dass a majalisar dokokin jihar Bauchi, Maryam Garba Bagel, ta koka a kan yadda ta ce wasu mutane na barazana ga rayuwar ta saboda dalilan siyasa.

Da take ganawa da manema labari yau, Talata, a gidanta, Maryam ta bayyana ta samu kira ranar Litinin daga wata lamba bayan ta dawo gida daga gidan ‘yar uwarta inda aka sanar da ita cewar ta duba kofar gidnta akwai wani kunshin takardu da aka ajiye.

Maryam ta cigaba da cewa, “bayan na kira mai tsaron lafiya ta na sanar da shi maganar kunshin takardun sai ya tabbatar min da cewar an kawo min wasu kunshin takardu. Abinda na gani cikin takardun ya matukar girgiza ni. Hotuna na ne aka yi masu wata hikima tamkar ni ce a jiki amma tsirara tare da wata nadaddiyar hira da ban san da ita ba.”

Ana yiwa rayuwata barazana saboda siyasa – ‘Yar majalisa Maryam Bagel
‘Yar majalisa Maryam Bagel

‘Yar siyasar ta kara da cewa daga baya ta kara samun wani kiran tare da gargadinta kan cewar muddin ba ta daina yiwa gwamnatin jihar Bauchi karkashin gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar adawa ba za a koya mata hankali.

Bayan na shaidawa mai maganar cewar ya yi duk abinda ya ga dama sai aka koma turomin wasu hotuna da nadadden sauti tare da yi mi barazanar cewar suna da duk wata shaida da zasu iya lalata min siyasa da rayuwa baki daya,” a cewar Maryam.

DUBA WANNAN: Hotunan bikin diyar gwamna Fayose mai barin gado

‘Yar majalisa Maryam na daga cikin ‘yan takarar da suka nemi maye gurbin Sanata da aka yi a jihar Bauchi sati biyu da suka wuce.

Maryam ta fita daga jam’iyyar APC ne gabanin zaben maye gurbin tare da komawa jam’iyyar SDP inda tayi takarar kujerar sanatan Bauchi ta kudu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel