Kwankwaso yayi bikin babbar sallah a wajen yawon neman shugaban kasa
Mun samu labari cewa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso yayi sallar sa ne a Kudancin Najeriya inda yake cigaba da zagaye domin neman goyon bayan jama’a game da 2019.

Kamar yadda mu ka samu labari, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayi bikin babbar sallah a Garin Benin da ke cikin Jihar Edo. Tsohon Gwamnan yayi sallah ne tare da Mabiya Kwankwasiyya da ke Yankin na Kudancin Najeriya.
Kafin nan kuma Sanata Kwankwaso wanda ya bar Jam’iyyar APC kwanaki ya dawo PDP ya kuma ziyarci fadar Oba na Benin Omo N’Oba N’Edo Uku’ Akpolokpolo Ewuare 11 domin tattauna wasu abubuwa da su ka shafi kasar nan.
KU KARANTA: An nadawa wani Gwamnan Arewa sarauta a bikin idi
Wani Hadimin tsohon Gwamnan na Kano Hon. Saifullahi Hassan ya bayyana cewa Rabi’u Kwankwaso ya gana da Sarkin Nufawa Alhaji Umar Yabagi da kuma Sarkin Hausawa Alhaji Adamu Sheikh Abdulrazak na Jihar Edo.
Kwanaki kun ji labari cewa tsohon Gwamnan Kano Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara zuwa fadar Oba na Benin. Ana tunani Kwankwaso na shirin tsayawa takarar Shugaban kasa ne karkashin Jam’iyyar adawa ta PDP.
Dazu labari ya zo mana cewa Mai girma Gwamna Nasir El-Rufai ya kafa tarihi a Jihar ta Kaduna a wannan babbar sallar inda aka nada sa a matsayin Garkuwan Talakawa na Yankin Jema’a.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng