An kashe mai kerawa 'yan tadda bam
Rahottani daga jami'an gwamnatin Amurka ya nuna cewa anyi nasarar kashe gagararren mai kerawa 'yan kungiyar ta'addanci na al-Qaeda bama-bamai a yankin Larabawa, Ibrahim al-Asiri kamar yadda BBC ta wallafa.
Kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito cewa wani jami'in da ya bukaci a boye sunansa yana cewa anyi amfani da jirgi mara matuki wato 'drone' wajen kashe dan a yammacin kasar Yemen.
An kuma bayyana cewa asalinsa dan kasar Saudiyya ne wanda ya yi
![An kashe mai kerawa 'yan tadda Bam An kashe mai kerawa 'yan tadda Bam](https://cdn.legit.ng/images/1120/vllkyt104c0quhfv48.jpeg?v=1)
Ana kyautata zaton cewa Asari ne ya kera bam din da wani dan Najeriya, Umar Farouk Abdulmutallab ya sanya cikin wandonsa a shekarar 2009 inda ya yi nufin tayar da bam din cikin jirgin sama amma aka kama shi
DUBA WANNAN: Ihu bayan hari: Hadimai na sun yi murabus ne saboda ina shirin sallamar su - Gwamna Tambuwal
Bayanan sirri da Amurka ta tattaro sun nuna cewa ya hada wasu bama-bamai da za a rika sanya wa a kwamfyuta ne hakan yasa Amurka ta hana shiga jirage da na'ura mai kwakwalwa.
Sakon da aka samu daga Al-Asiri wata sakon murya ce a shekarar 2016 inda ya yi barazanar kaiwa saudiyya da Amurka hari bayan Saudiyya ta ahala 'yan al-Qaeda 47 da ake zargi da ayyukan ta'addanci.
A makon jiya, majalisar dinkin duniya ta fitar da wani rahoto da ke cewa watakila an kashe Asiri tare da cewa kisan mai hada bama-baman zai karya lagwan ayyukar kungiiar al-Qaeda sosai a yankin Larabawa.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng