Yanzu mutane sun fahimci cewa Shugaba Buhari garau yake – Garba Shehu

Yanzu mutane sun fahimci cewa Shugaba Buhari garau yake – Garba Shehu

Dazu ne Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nunawa Duniya cewa har yanzu yana cikin koshin lafiya bayan da yayi wata doguwar tafiya bayan ya sauko da masallaci wajen sallar idi a Garin Daura.

Yanzu mutane sun fahimci cewa Shugaba Buhari garau yake – Garba Shehu
Buhari ya nunawa Tambuwal cewa karyar sa ta sha karya

Shugaban kasar yayi watsi da tsarin da aka shirya masa na hawa mota ya koma gida inda ya taka da kafar sa har na tsawon kusan kilomita guda. Hakan dai ya zama martani ga masu cewa Shugaban ya tsufa da mulkin kasar nan.

Mai magana da yawun bakin Shugaban kasa watau Garba Shehu yace tafiyar da Buhari yayi ta nuna cewa lafiyar sa kalau. Hadimin Shugaban kasar yace yanzu jama’an da ke hangen kujerar sa sun gane cewa Buhari garau yake.

KU KARANTA:

Shehu ya kuma bayyana cewa masu neman mulkin kasar nan saboda kuruciya da koshin lafiyar su sai su gane cewa hakan ba zai kai su ko in aba. Mai magana da yawun Shugaban yace sai kuma ‘Yan takarar su tari wani abin dabam.

Malam Garba Shehu ya kuma bayyana cewa tattakin da Shugaban kasa Buhari yayi ya nuna cewa shi mutum ne mai kaunar masoyan sa ganin yadda ya fito daga motar domin jama’a su hange shi. Dazu ne dai Buhari yayi sallar idi a Daura.

Dama kun ji cewa Gwamna Aminu Waziru Tambuwal wanda ake tunani yana cikin masu neman kujerar Shugaban kasa ya nuna cewa Shugaba Buhari bai da isasshen lafiyar mulkin kasar nan.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel