Abin da ya sa ba zan bar Jam’iyyar APC ba – inji Gwamna Bindow

Abin da ya sa ba zan bar Jam’iyyar APC ba – inji Gwamna Bindow

Mun ji labari cewa Gwamnan Jihar Adamawa Bindow Jibrilla ya tabbatar da cewa ba shi da niyyar sauya-sheka ya bar Jam’iyyar APC mai mulki. Kwanaki dai Atiku Abubakar da dinbin Mabiyan sa su ka bar APC a Jihar Adamawa.

Abin da ya sa ba zan bar Jam’iyyar APC ba – inji Gwamna Bindow
Gwamna Bindow yace ba zai bar Jam'iyyar APC mai mulki

Gwamnan Adamawa wanda ba mamaki ya nemi tazarce a 2019 yace babu abin da zai sa ya bar Jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan, Gwamnan yana mai cewa a APC zai cigaba da zaman sa har ya gama rayuwar siyasar sa.

Bindow Jibrilla ya ki barin Jam’iyyar APC duk da wanda ake tunani shi ne uban gida sa ya koma PDP. A 2015 Atiku Abubakar yana cikin wanda su kayi sanadiyyar Bindow ya zama Gwamnan Jihar Adamawa a Jam’iyyar APC mai mulki.

KU KARANTA: Shugaba Buhari ya yanka rahon layya a Daura

Gwamnan ya bayyana cewa tarayyar sa da kokarin marawa Shugaba Buhari baya ne zai hana sa barin APC. Gwamnan yake cewa zai marawa Buhari baya domin ganin ya samu zarcewa a kan kujerar mulki a zabe mai zuwa na 2019.

Gwamna Bindow Jibrilla ya kuma nemi Mukarraban sa da sauran manyan APC su yi kokari wajen ganin an marawa Gwamnatin sa baya tare da kokarin ganin Jam’iyyar APC da Shugaban kasa Muhammadu Buhari sun lashe zabe mai zuwa.

Kamar yadda labarin ya zo mana, Gwamnan yayi wannan jawabi ne wajen wani taron Majalisar zartarwa na musamman na Jihar inda yake fadawa Mukarraban sa cewa Shugaba Buhari yana nufin Yankin su na Arewa maso gabas da alheri.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel