Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyar ADC ta samu cikin kankanin lokaci

Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyar ADC ta samu cikin kankanin lokaci

Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya shawarci jam'iyyar ADC ta kada ta maimaita irin kura-kuren da sauran jam'iyyun Najeriya su kayi saboda hakan ne zai sa ta ware kanta daga cikinsu.

A jawabin da ya yi yayin da yake maraba da tawagar kwamitin gudanarwa na ADC karkashin jagorancin Ciyaman dinsu, Cif Ralphs Nwosu a jiya a Abeokuta, Obasanjo ya ce cikin kankanin lokaci jam'iyyar ta kasance cikin jam'iyyu da ake girmamawa.

Ya bukaci jam'iyyar ta cigaba da kasancewa jam'iyya mai tafiya tare da kowa tare da kare hakkin mambobinta kuma ta cigaba da kasancewa jam'iyyar da mambobin ne ke tafiyar da harkokinta ba tsirarun mutane masu kudi ba.

Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyarsa (ADC) ta samu cikin kankanin lokaci
Obasanjo ya lissafa nasarorin da sabuwar jam'iyyarsa (ADC) ta samu cikin kankanin lokaci

DUBA WANNAN: Bikin Sallah: Gwamna Tambuwal ya yiwa marayun Sakkwato sha tara na arziki

Obasanjo yace idan jam'iyyar ta cigaba a haka, zasu kasance jam'iyyar mai nagarta ba kamar wasu jam'iyyun da wasu tsiraru ke amfani da kudin gwamnatin wajen tafiyar da harkokin jam'iyyar ba.

Obasanjo na sake nanata cewa shi ba dan jam'iyyar ADC bane amma a shirye yake ya rika basu shawarwari a duk lokacin da suke bukuta tare da cewa yana muran da kafuwar jam'iyyar saboda yanzu mutane suna da zabi bayan APC da PDP.

Tsohon shugaban kasan ya cigaba da cewa manyan jam'iyyun Najeriya suna fama da matsaloli daban-daban da wanda suka hada da rashin jagoranci na gari da rashin kishi tsakanin mambobin amma muddin ADC ta cigaba kan turbar gaskiya da adalci zata kasance itane jam'iyyar da zata mamaye kasar.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel