Cikin EFCC ya duri ruwa, an kai ta kara ana bukatar ta biya diyyar Naira N50b

Cikin EFCC ya duri ruwa, an kai ta kara ana bukatar ta biya diyyar Naira N50b

- Yau an kai mai kaiwa kotu kara kuma har ana bukatar ya biya diyya

- Bayan kullewa jihar Akwa Ibom asusunta, jihar ta dauki matakin shari'a

- Har ma tana sanya ran samun nasara gaban alkali

Gwamnatin jihar Akwa Ibom ta gurfanar da hukumar EFCC tare da wasu bankuna a gaban wata babbar kotun daukaka kara dake da mazauni a Uyo bisa zarginsu da dakatar da gwamanatin jihar yin amfani da wasu kudade da yawansu ya kai Naira biliyan hamsin, wanda yin hakan ba ya bisa doka.

Cikin EFCC ya duri ruwa an kai ta kara ana bukatar ta biya Diyyar Nair N50b.
Cikin EFCC ya duri ruwa an kai ta kara ana bukatar ta biya Diyyar Nair N50b.

Babban mai shari'a kuma kwamishinan shari'a na nihar ta Akwa Ibom Uwemedimo Nwoko ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai a cikin karshen makon da ya gabata.

Ya kara da cewa gwamnatin jihar Akwa Ibom ta yanke hukuncin kawo karshe wannan al'amarin ta hanyar bin doka, domin hukumar EFCC bata da hurumin dakatar asusun ajiyar kudin jihar.

kwamishinan ya shaida cewa “Mun garzaya kotun domin ta fayyace mana tare kuma da tabbatar mana da wasu bayanai da za su zama madogara a garemu”.

KU KARANTA: Koda PDP ce ta samu nasara a 2019 zamu yarda – Osinbajo

"Shin ko asusun ajiyar kudin Jjhar Akwa Ibom ya fada cikin tanadin dokar kundi sashe na 34 na hukumar ta EFCC na shekara ta 2004".

Kan ya kara da “Na tabbata zamu yi nasara a gaban kotu, domin kuwa babu ko tantama wannan mataki da hukumar EFCC ta dauka ba ya bisa doka, don ko a cikin kundin tsarin mulkin kasar nan babu wani guri da yayi tanadin hakan".

“Kuma ko da hukumar EFCC tana gudanar da bincike ne da ya shafi almundahanar kudi, ko da an samu zargin yana da tushe, to babu shakka hukumar bata da hurumin rufewa ko dakatar da shige da ficen kudi a cikin asusun gwamnatin jihar". Uwemedimo Nwoko ya jaddada.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel