Babbar Sallah: Matar Gwamna Kashim Shettima ta yi rabon raguna 100 ga Malamai da gajiyayyu
Hajiya Nana Shettima, uwargidar gwamnan jihar Borno, Kashim Shettima ta yi ma wasu Malamai da mata gajiyayyu kabakin arziki a ranar Lahadi, 19 ga watan Agusta a garin Maiduguri na jihar Borno.
Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Hajiya Nana ta raba raguna guda dari ga wasu zababbun Malaman addinin Musulunci da wasu matan da suka rasa mazajensu a sanadiyyar rikicin Boko Haram.
KU KARANTA: Alkalumman tarin dukiya da rayukan jama’a da aka yi asara sakamakon rikicin jihar Zamfara
Majiyar Legit.ng ta ruwaito Hajiya Nana ta gudanar da wannan aikin alheri ne ta karkashin wata gidauniyarta da ta kirkira don tallafa ma marayu, mata gajiyayyu da kuma Malaman makarantun allo, wato Support for Widows, Orphans and Tsangaya (SOWT) Foundation, a turance.
Nana tace ta bada wannan tallafi ga wadanda suka amfana ne don su samu abinda zasu yanka a yayin bikin babbar Sallah dake karatowa, sa’annan ta bukacesu dasu taimaka ma Najeriya da addu’ar samun zaman lafiya mai daurewa.
“Wannan tallafi na bada shi ne don taimakonsu albarkacin bikin Sallah babba.” Inji ta. Ita ma wata mata daga cikin wadanda suka amfana, Yagana Mustapha ta gode ma uwargidar gwamna game da wannan rago, inda tace da wannan zata gudanar da Sallah cikin farin ciki da kwanciyar hankali.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng