Masana’antar Kannywood: Jarumin fina-finan Hausa ya rasu

Masana’antar Kannywood: Jarumin fina-finan Hausa ya rasu

Allah ya yiwa Ayuba Dahiru da aka fi kira Tandu, jarumi a masana’antar shirya finan-finan Hausa dake Kano, rasuwa.

Da sanyi safiyar yau, Lahadi, ne marigayin ya rasu a garin Kano fayan fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda dareka a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi, ya shaidawa BBC Hausa.

Allah ya yiwa Ayuba Tandu rasuwa bayan ya sha fama da zazzabi na kwana biyu. Muna masu addu’ar Allah ya gafarta masa,” in ji Falalu Dorayi.

Masana’antar Kannywood: Jarumin fina-finan Hausa ya rasu
Marigayi Ayuba Tandu

DUBA WANNAN: INEC ta bayyana dalilin da yasa ba zata daga zaben 2019 ba

Kafin rasuwar sa, Tandu ya fi fitowa a fina-finai ko matakin barkwanci. Wasu daga cikin fina-finan day a fito sun hada da Auren Manga da Gobarar Titi da kuma Afrah.

Ya rasu ya bar mata uku da kuma yara 9.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Online view pixel