Tsoron yagewar lema: PDP ta fara tunanin fitar da dan takarar sasanto daga cikin ‘yantakara 12
Wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar PDP da suka da makomarta bayan kammala zaben dan takarar shugaban kasa da zata yi ranar 5 ga watan Oktba, sun fara neman yadda za a fitar da dan takara ta hanyar sulhu tare da fara neman dan takarar sasanto da za a saka gaba.
Masu kokarin kare wannan tunani na ganin ta hakan ne kadai jam’iyyar zata kaiwa ga zabukan shekarar 2019 a dunkule, kamar yadda jaridar The Nation ta rawaito.
A yanzu haka akwai ‘yan takarar shugaban kasa mutum 11 a jam’iyyar ta PDP. Sun hada da tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, gwamnan jihar Kano, Aminu Waziri Tambuwal, gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo na jihar Gombe, tsohon ministan harkoki na musamman, Tanimu Turaki da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Sanata Ahmed Makarfi.
Akwai tsoffin gwamnonin jihar Kano, Ibrahim Shekarau da Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Sokoto, Attahiru Bafarawa, takwaransa na jihar Jigawa, Sule Lamido, da kuma dan gwagwarmaya Dakta Baba Datti Ahmed.
A ranar Talata da ta gabata ne shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, ya bayyana cewar yana tuntuba da matukar nuna yiwuwar shiga cikin masu son jam’iyyar PDP ta tsayar das u takarar shugaban kasa.
Jam’iyyar PDP ta tsayar da ranakun 5 da 6 ga watan Oktoba domin taron fitar da dantakarar shugaban kasa da zai wakilce su a zaben watan Fabrairu na 2019.
An fara ganin alamun jam’iyyar na son yin sulhu ne ta bakin Walid Jibrin, shugaban kwamitin amintattu wanda ya bayyana damuwarsa da yawan da ‘yan takara ked a shi tare da sanar da cewar: “akwai kokarin ganin mun hada kan ‘yan takarara mu gaba daya domin ganin sun hada kai domin amincewa da dan takara guda da zai mana takararar shugaban kasa.”
DUBA WANNAN: Zaben maye gurbi a jihar arewa: PDP ta kayar da APC
Sannan ya kara da cewa, "muna da mutane masu kima da mutuncin da ba zasu taba saka son rai ba wajen fitar da sahihin dan takarar shugaban kasa sahihi ba".
PDP na tsoron makomar jam’iyyar muddin ta bari aka kai ga matakin fitar dan takara ba tare da tayi kokarin tsoma baki ba. Lamarin da take ganin muddin bata shawo kansa yanzu ba kan iya kaiwa ga fatattakewar lemar da ‘ya’yanta ke tsaye karkashi.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng