Sojojin Najeriya sun yi bajinta, an basu lambar yabo

Sojojin Najeriya sun yi bajinta, an basu lambar yabo

- Bayan nuna hazaka a gasar da aka sanya tsakanin Sojoji, an girmama wadanda suka yi bajinta

- Gasar dai an shirya ta ne don kara dankon zumunci tare da karawa Sojojin kwarin gwiwa

Wasu jami'an Sojojin kasar nan guda 4 sun yi nasarar lashe lambobin Azurfa a gasar wasanni da ta guda a tsakanin dakarun Sojin kasar nan a barikin Ekehuan dake jihar Benin.

Tun da farko dai Barikin Sojoji ta birnin Edo ce ta dauki bakunci gasar wacce ta gudana a tsakankanin kananan Sojoji tare da manyan Sojojin.

Sojojin Najeriya sun yi bajinta, an basu lambar yabo
Sojojin Najeriya sun yi bajinta, an basu lambar yabo

Gasar wacce aka fara ta ranar 13 ga watan Agusta zuwa ranar 17 ga watan Agustan nan, an yi wasanni wadanda suka hadar da harbin bindiga da tsalle-tsalle da kuma wasanni motsa jiki.

Da yake tsokaci dangane da yadda gasar ta gudana, Manjo Janaral O. F Azinta wanda shi ne babban kwamandan barikin Sojojin, ya yabawa wadanda suka yi nasarar lashe kyaututtikan tare da bayyana gamsuwarsa akan yadda aka gudanar da gasar.

KU KARANTA: ‘Yan sanda sun yi namijin kokorin kama ‘yan bindiga 20 da makamai masu yawa a Zamfara

“Shirya wannan gasar babban muhimmin abu ne a tsakankanin matasan sojoji, domin hakan zai kara tayar musu da kwarewarsu tare da nuna hazakarsu" In ji Manjo janaral O. F Azinta.

Daga nan ne kwamandan ya kara da cewa “Gasar nan za ta kara hada kan jami'an Sojoji waje guda wanda hakan zai Kulla kyakykyawar dangantaka a tsakaninmu".

Gasar dai ta samu bakunci Sojoiji daga barikokin Sojojin dake fadin kasar nan, wadanda suka hadar da barikin Sojoji da ke Ilorin da na Akure da kuma Ibadan.

An kuma gudanar da wasanni nau'i daban- daban, kamar wasan harbi, da Ninkaya da guje-guje da Tsalle-tsalle da sauran wasanninn motsa jiki.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel