Ministan harkokin mata Alhassan ta sha da kyar a Jihar Taraba

Ministan harkokin mata Alhassan ta sha da kyar a Jihar Taraba

Mun samu labari daga Jaridar Daily Trust cewa Ministan harkokin mata Hajiya Jummai Alhassan, ta sha da kyar a wani Kauye a Jihar Taraba lokacin da ta kai ziyara a Jihar ta a karshen makon nan.

Ministan harkokin mata Alhassan ta sha da kyar a Jihar Taraba
An nemi a ga bayan Ministan harkokin mata a Taraba

Wasu ‘Yan iskan gari sun kai hari ga tawagar Ministar mata ta Najeriya a Garin Takum da ke cikin Jihar Taraba. Wannan abu maras dadi ya auku ne a cikin Anguwan Dogo inda ake tunani Jam’iyyar APC na da karfi sosai.

Kamar yadda labarin ya zo mana, wasu matasa sun yi kaca-kaca da motocin da ke cikin tawagar Ministar kasar inda har ta kai aka yi kaca-kaca da motar ofishin Hajiya Jummai Alhassan mai lambar AE89 SDA.

KU KARANTA: Shugaba Buhari zai marawa Ministar sa baya ta tsige PDP a Taraba

Wasu tsagera ne dai a Garin na Takum su ka hana Ministar wucewa ta wata hanya su ka kuma yi mugun barna. Sanata Jummai Alhassan wanda ta nemi Gwamna a Jihar a 2015 tace wannan danyen aiki bai bata mamaki ba.

Ministar ta zargi ‘Yan adawan ta da kitsa wannan mugun aiki inda tace dama ta ji kishin-kishin din cewa an dauko hayar ‘Yan iskan gari domin su shirya mata wannan manakisa. ‘Yan Sanda ne dai su ka kawo dauki a lokacin.

Mai magana da yawun ‘Yan Sanda a Jihar Taraba David Misal yace ba su san da wannan labari ba. Kwanan nan ne dai aka yi wani zabe domin cike gurbin ‘Dan Majalisar na Yankin Takum da aka kashe a shekarar bara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel