2019: Manyan ‘Yan siyasar Jihar Oyo sun sha alwashin ba APC kunya

2019: Manyan ‘Yan siyasar Jihar Oyo sun sha alwashin ba APC kunya

Mun ji labari cewa a Jihar Oyo da ke Kudancin Najeriya an hada kai tsakanin manyan Jam’iyyun adawa da kuma wadanda su ka balle daga APC domin a tika Jam’iyyar mai mulki da kasa a zaben 2019 a karkashin Jam’iyyar adawar nan ta ADC.

2019: Manyan ‘Yan siyasar Jihar Oyo sun sha alwashin ba APC kunya
Manyan ‘Yan siyasar Oyo sun koma ADC ta su Obasanjo. Hoto: Daily Trust

Daily Trust ta bayyana cewa manyan Jam’iyyar LP watau Labor Party da wasu tsofaffin ‘Yan Jam’iyyar APC a sun hada karfi da karfe domin ba APC kashi a Jihar Oyo. Akwai tsofaffin Gwamnoni da Mataimakan su da duk sun dawo ADC.

Daga cikin wadanda ke wannan shiri akwai ‘Yan Majalisar dokokin Jihar Oyo har mutane 16 wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Wasiu Musa yake jagoranta. Sauran manyan PDP a da irin su Rashidi Ladoja su na cikin wannan tafiya a Jihar.

KU KARANTA: Manyan abubuwa 4 da ke gaban Shugaba Buhari kafin zaben 2019

Akwai wasu tsofaffin Sakatarorin Gwamnan Jihar Oyo har 5 da su ke cikin Jam’iyyar ADC, wadannan tsofaffin SSG sun hada da: Dr. Busari Adebisi, Cif Michael Koleoso, Cif Sarafadeen Abiodun Alli, Cif Olayiwola Olakojo da Dele Adigun.

Hammed Gbadamosi da kuma Taofeek Arapaja wadanda sun taba rike mukamin Mataimakin Gwamna a Jihar ta Oyo sun sha alwashin tika APC da kasa a 2019. Daga cikin wanda su ke cikin Jam’iyyar ta ADC kuma akwai Sanata Monsurat Sunmonu.

Har wa yau akwai wasu jiga-jigan siyasa a Oyo irin su Dapo Lam Adesina, Gbenga Babalola da Olufemi Lanlehin da su ke neman tunbuke APC a 2019. Manyan PDP a Jihar da wasu tsofaffin Kwamishinoni da dama duk sun sauya-sheka zuwa ADC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel