'Yan sanda a jihar Katsina sun yi babban kamu

'Yan sanda a jihar Katsina sun yi babban kamu

Hukumar 'yan sandan Najeriya reshen jihar Katsina sun yi shelar kama wasu kwararrun masu aikata fyade da ta'ammali da miyagun kwayoyi da suka dade suna lalata rayuwa da tarbiya a jihar.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Katsina, Mohammed Wakili, ya sanar da hakan yau Laraba yayin yayin bajakolin masu laifin ga manema labarai a shelkwatar hukumar dake garin Katsina.

Daga cikin wadanda aka kama din akwai Sani Haruna; mai shekaru 30, da Nura Ibrahim; mai shekaru 26 dukkan su mazauna kauyen Unguwar Gambo dake karamar hukumar Malumfashi. Ana tuhumar su aikata laifin fyade ga wata karamar yarinya mai shekaru 9 tare da yi mata raunuka a al'aurar ta.

Ragowar masu aikata laifin fyade da aka kama akwai Abdulrashid Dalha, mai shekaru 55 dake zaune a kauyen Dajin Mare dake karamar hukumar Dandume. Ana tuhumar sa da yiwa wata yarinya mai shekaru 8 fyade a wani kango da kuma wani Abdullahi Sani mai shekaru 25, mazaunin kauyen Unguwar Namama dake karamar hukumar Dandume. Ana tuhumar sa da yiwa wata yarinya mai shekaru 7 fyade yayin da je jeji domin yanko ciyawa.

'Yan sanda a jihar Katsina sun yi babban kamu
'Yan sanda

Kazalika, hukumar ta gabatar da wani Jabiru Ahmed mai shekaru 25 dake zaune a kauyen Dutsen-Reme a karamar hukumar Bakori wanda ake tuhuma da lalata wata yarinya mai shekaru 4 a dakinsa.

Hukumar ta bayyana kama wasu mutane biyu, Hassan Muhammad mai shekaru 22 da Umar Yusuf mai shekaru 23, da laifin sayar da kodin a cikin garin Katsina.

DUBA WANNAN: Babbar Magana: Kotu ta yiwa babban sufetan ‘yan sanda albishir da tura shi gidan yari

Kwamishinan na 'yan sanda ya bayyana cewar hukumar tayi nasarar kama wasu barayin shanu a karamar hukumar Batsari.

Barayin shanun da aka kama sun hada da: Zaharaddin Rabi'u mai shekaru 21 dan asalin kauyen Dumburum dake jihar Zamfara, Nura Musa mai shekaru 31 da Jamilu Gambo mai shekaru 30, dukkan su 'yan asalin karamar hukumar Jibia.

Har ila yau hukumar ta gabatar da wani mutum, Steven Yakubu mai shekaru 67, wanda ke damfarar mutane ta hanyar yin sojin gona da cewar shi tsohon Birgediya janar ne a hukumar soji.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel