Bikin Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Ma'aikata Albashin watan Agusta a jihar Kano

Bikin Sallah: Gwamna Ganduje zai biya Ma'aikata Albashin watan Agusta a jihar Kano

Da sanadin rahoto na shafin jaridar Premium Times mun samu cewa, gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya bayar da umarni na biyan albashin watan Agusta ga ma'aikatan jiha da na kananan hukumomi dake garin Kano.

Cikin wata sanarwa da sa hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Muhammad Garba ya bayyana cewa, gwamna Ganduje yayi wani hobbasa ta son barka domin baiwa ma'aikatan sa dama ta gudanar da shagulgula na bikin babbar Sallah cikin annashuwa tare da iyalan su.

Yake cewa, wannan yunkuri na daya daga cikin tsayuwa da sadaukarwar gwamnan na inganta jin dadin ma'aikata a jihar ta Kano.

Mallam Garba yana kuma sa ran ma'aikatan za su yi koyi da wannan kyautatawa ta gwamnatin jihar wajen zage dantsen su na sauke nauyin da rataya a wuyan su a yayin gudanar da ayyuka a ma'aikatun su.

KARANTA KUMA: Cikin Hotuna: Osinbajo ya ziyarci wurin da Gini ya rushe a garin Abuja

Kwamishinan ya na kuma taya ma'aikatan murnar wannan biki tare da addu'ar Allah maimaita inda ya kuma neme su akan su jajirce wajen mika kokon su na barar addu'a ga Mahalicci domin ya wanzar da zaman lafiya da ci gaba a jihar.

Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, Gwamnatocin jihohin Sakkwato da Kebbi sun yi makamanciyar wannan abin son barka ga ma'aikatan su tun a makon da ya gabata.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a zaurukan sada zumunta kamar haka:

https://www.business.facebook.com/naijcomhausa

http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel