Kundin Kannywood: Yanda Rarara yayi min hanyar shiga wasan Hausa - Hauwa Mama

Kundin Kannywood: Yanda Rarara yayi min hanyar shiga wasan Hausa - Hauwa Mama

Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Hauwa S. Garba wacce aka fi sani da 'Mama' tana daya daga cikin wanda tauraruwar su ke haskawa a 'yan wasan Hausa a yanzu

Yanda Rarara yayi min hanyar shiga wasan Hausa - Hauwa Mama
Yanda Rarara yayi min hanyar shiga wasan Hausa - Hauwa Mama

Fitacciyar 'yar wasan Hausan nan Hauwa S. Garba wacce aka fi sani da 'Mama' tana daya daga cikin wanda tauraruwar su ke haskawa a 'yan wasan Hausa a yanzu.

A zantawar da manema labarai suka yi da ita, yarinyar 'yar shekara 19, kuma haifaffiyar jihar Legas, ta bayyana irin abubuwan da suka ja ra'ayinta ta shiga harkar fim din Hausa.

DUBA WANNAN: An samu nasarar ceto mutane bakwai daga benen da ya rushe a Abuja

'Yar wasan ta bayyana yanda ta tsinci rayuwar ta cikin shirin fim din Hausa. Tace ta tsinci kanta a cikin shirin fim din Hausa ne a lokacin da ta hadu da shahararren mawakin nan na siyasa, Dauda Kahutu Rarara. Ta ce kafin ta hadu da Rarara, tana zaune da Aunty ta a jihar Kano.

Mu ma'abota kalon shirin fim din Hausa ne, ta dalilin haka naji wasan ya fara kwanta mini a rai, kuma naji ina sha'awar shiga harkar. Bazan manta ranar da muke hirar 'yan fim din Hausa da wata 'yar uwata, na fada mata cewar ina sha'awar shiga harkar fim. Sai take ce mini ai ta san Rarara, daga nan tayi minijagora zuwa wurin shi.

Da muka hadu dashi sai yake fada mini cewar shi baya shirin fim, amma zai hada ni da wani wanda ya sani. Ba a dade ba ya hadani da shahararren mai shirya fina-finan Hausan nan Usman Mu'azu. TO tun daga nan na fara fitowa a shirin fim din Hausa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng