'Yan wasan Najeriya 5 da ake tunanin zasu mara wa Victor Moses baya

'Yan wasan Najeriya 5 da ake tunanin zasu mara wa Victor Moses baya

Idan ba a manta ba mun kawo muku labarin cewar fitaccen dan wasan kwallon kafan nan na Najeriya, Victor Moses, ya yi murabus daga bugawa Najeriya wasa

'Yan wasan kwallon kafa 5 da ake tunanin zasu mara wa Victor Moses baya
'Yan wasan kwallon kafa 5 da ake tunanin zasu mara wa Victor Moses baya

Idan ba a manta ba mun kawo muku labarin cewar fitaccen dan wasan kwallon kafan nan na Najeriya, Victor Moses, ya yi murabus daga bugawa Najeriya wasa, domin ya mai da hankali wurin bugawa kungiyarsa wasa.

A yanzu haka dai 'yan Najeriya suna ta fitar da sunayen 'yan kungiyar kwallon kafar Najeriyan, wanda ake tunanin zasu bi bayan dan wasan, ma'ana suma zasu daina bugawa Najeriya wasa. A cikin jerin 'yan wasan da ake saka ran zasu yi koyi da Victor Moses din akwai:

DUBA WANNAN: An kai mummunan hari masallatan juma'a guda 2 a lokaci daya

1. Ahmed Musa: Wanda ya fi kowa zura kwallaye a gasar kofin duniya da aka buga a bana a kasar Rasha, wanda a yanzu haka wata kungiya a kasar Saudiyya mai suna Al-Nassr FC ta siye shi a wurin kungiyar Leicester, domin ya dinga buga mata wasa.

2. Mike Obi: Dan wasan wanda yanzu haka yake zaune a kasar China, ya sha fama da 'yan Najeriya da irin yanda yake buga wasan shi, ya samu damar yin suna ne a lokacin da yaje gasar cin kofin duniya na matasa a shekarar 2005.

3. Odion Ighalo: Dan wasan gaban kungiyar Changchun Yatai, mai shekaru 29, 'yan Najeriya baza su taba mancewa dashi ba, saboda kusan dalilin shi yasa Najeriya ta fadi wasan da aka buga tsakanin ta da kasar Argentina a gasar cin kofi duniya da aka buga bana a Rasha.

4. Ogenyi Onazi: Ya shiga cikin kungiyar kwallon kafa ta Najeriya tun yana dan shekara 16, inda ya wakilci Najeriya a gasar cin kwallon kafa na kasa da 'yan shekara 17, wato U-17, inda dalilin haka ya samu damar shiga babbar kungiyar a shekarar 2012.

5. Joel Obi: Dan wasan dan shekara 27, ya samu yin suna a duniya a shekarar 2011 a wani wasa da Najeriya ta buga da kasar Sierra Leone a jihar Legas, bayan haka kuma dan wasan ya samu damar zuwa gasar cin kofin duniya da aka buga bana a kasar Rasha.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng