Jihar Gombe na fitar da Macizai 400 zuwa 'Kasar Ingila a kowane Wata

Jihar Gombe na fitar da Macizai 400 zuwa 'Kasar Ingila a kowane Wata

Da sanadin shafin jaridar Premium Times mun samu rahoton cewa, jihar Gombe dake Arewacin Najeriya ta yi kaurin suna wajen cin kasuwar macizai inda take fitar da fiye da guda 400 na nau'ika daban-daban zuwa kasar Ingila a kowane watan Duniya.

Cibiyar kula da kuma magance cizo da harbin macizai dake garin kaltungo a jihar Gombe ke gudanar da wannan lamari na safarar macizai zuwa wata cibiya makamanciyar ta dake birnin Liverpool a kasar ta Ingila.

Shugaban wannan cibiya, Abubakar Ballah, shine ya bayyana hakan yayin ganawa da manema labarai cikin garin Kaltungo a ranar Alhamis din da ta gabata, inda ya ce ana amfani da wannan macizai ne wajen hada kwayoyi da sunadaran magance dafi na harbi da kuma cizon su.

Yake cewa, kasar ta Ingila ta tatsar dafin macizan wajen hada magunguna inda take sayarwa da Najeriya akan farashi mai rahusa akan N35, 000 kacal sakamakon wannan gudunmuwa da take bayarwa.

Jihar Gombe na fitar da Macizai 400 zuwa 'Kasar Ingila a kowane Wata
Jihar Gombe na fitar da Macizai 400 zuwa 'Kasar Ingila a kowane Wata

Sai dai Ballah ya bayyana cewa, ana sayar da magungunan akan farashi mai tsadar gaske na Dalar Amurka 1900 kimanin N684, 000 a kudin Najeriya ga sauraran kasashe da ba su bayar da gudunmuwar macizai ga kasar ta Ingila.

A cewar sa, ana kuma sayar da wannan nau'ikan magunguna akan kimanin Naira miliyan bakwai zuwa takwas a kasar Amurka inda ya dara ko ina tsada a fadin duniya.

Ya ci gaba da cewa, cibiyar na sayen kowane maciji guda akan Naira 500 zuwa 1000 gwargwadon girma inda ake aika su zuwa Birnin tarayya wanda daga nan sai a shilla da su zuwa kasar Ingila.

KARANTA KUMA: Hukumar 'Yan sanda ta damuƙe Masu neman Maza 6 a jihar Abia

Legit.ng ta fahimci cewa, a yayin isar wannan macizai kasar Ingila, an kuma duba tare da tantance lafiyar su domin tabbatar da rashin wahala ko tagayyara a tattare da su sakamakon kare hakkin dabbobi da kasar ta baiwa muhimmanci.

Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya ruwaito cewa, karamar hukumar Kaltungo dake jihar ta Gombe da shahara da sunan daular macizai sakamakon arziki na yawaitar nau'ikan wannan dabbobi a yankin dake Arewacin Najeriya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel