Anyi mummuman ambaliyar ruwan da ba a taba yi ba a wannan karnin a India

Anyi mummuman ambaliyar ruwan da ba a taba yi ba a wannan karnin a India

- Wani mummunan ambaliyar ruwa, wanda hasashe ya nuna ba a taba yin irin shi ba a wannan karnin ya cinye jihar Kerala dake kasar Indiya

- Mutane sama da 164 suka rasa rayukan su, sannan sama da mutane 200,000 suka rasa muhallin su

Anyi mummuman ambaliyar ruwan da ba a taba yi ba a wannan karnin a India
Anyi mummuman ambaliyar ruwan da ba a taba yi ba a wannan karnin a India

Wani mummunan ambaliyar ruwa, wanda hasashe ya nuna ba a taba yin irin shi ba a wannan karnin ya cinye jihar Kerala dake kasar Indiya, inda mutane sama da 164 suka rasa rayukan su, sannan sama da mutane 200,000 suka rasa muhallin su.

Firaministan kasar Narendra Modi ya samu damar kai ziyara wurin da abin ya shafa, inda yace yana fatan hukumomin tsaro na kasar zasu yi iya bakin kokarin su don ceto mutanen da abin ya shafa, inda a halin yanzu akwai jirage masu saukar ungulu sama da guda 10 da suke shawagi a jihar suna ceto al'umma tare da jiragen ruwa masu yawan gaske.

DUBA WANNAN: Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis

"Nayi magana da ministan tsaro na kasar nan akan a kawo karin wasu jiragen, domin kuwa wasu wuraren dole sai dai a janyo mutum da jirgin sama, saboda har yanzu akwai dubunnan mutane a wurin."

Ambaliyar ruwan ya fara afkuwa kwanaki tara da suka wuce, sannan Vijayan ya ce sama da mutane 164 sun rasa rayukan su sanadiyyar ambaliyar ruwan, haka kuma sama da mutane 223,000 sun rasa muhallan su.

Kerala jiha ce wacce baki suke tururuwan zuwa domin yawon bude ido. Amma sanadiyyar ambaliyar ruwan yasa aka rufe babban filin tashi da saukar jiragen sama na garin Kochi babban birnin jihar, saboda ruwa ya cinye filin, hukumar kasar tace za'a cigaba da rufe filin jirgin har zuwa ranar 26 ga wannan watan.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel