Kyawawan hotunan iyalan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, matarsa da yaransa

Kyawawan hotunan iyalan shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki, matarsa da yaransa

Iyalai sune komai na rayuwa kuma Allah ya mallakawa shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki iyali abun sha’awa. Kwanan nan ne uwargidansa, Toyin Saraki ta wallafa kyawawan hotunan iyalansu a shafinta na Instagram don murnar nasarar da suka samu a gidansu.

Da take godema Allah akan ni’imar da yayi asu ta bayyana cewa tagwayenta sun samu gurbin karatu a manyan jami’o’i domin karantar karatun likitanci.

Ta wallafa wasu baituka na bege ga Ubangiji cikin harshen gargajiya wato da yaren yarbanci.

KU KARANTA KUMA: Wata yarinya ta kuduri aniyar kare hakkin Fulani

Wadannan hotuna na iyalan Saraki yayi fice inda mutane suka nuna sha’awarsu ga wannan iyalai a shafukan zumunta.

Ga hotunan a kasa:

A baya Legit.ng ta rahoto cewa Shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki yace yana nazari akan yiwuwar tsayawarsa takarar shugaban kasa a zabe mai zuwa.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel