Ba zan iya aiki ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba - Wani Mutum ya shaidawa Kotu

Ba zan iya aiki ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba - Wani Mutum ya shaidawa Kotu

A ranar Alhamis din da ta gabata ne wata Mutum mai shekaru 34 a duniya, Joseph Mukindi Njeru, ya shaidawa wata Kotu ta Embu dake kasar Kenya cewa ba zai iya aikin sa na yasa da haƙa ramuka ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya bayyana, ana tuhumar wannan Matashi bisa laifi na mallakar ɗauri 16 na Tabar Wiwi a gaban Alkaliin Kotun ta Majistire, Maxwell Gicheru.

Sai dai Mista Joseph wanda aka cafke a ranar Talatar da ta gabata ya musanta zargin da ake yi a kansa da cewa, ya mallaki wannan tabar wiwi ne domin amfanin kansa ba don fataucin ta ga mabukata ba.

Ba zan iya aiki ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba - Wani Mutum ya shaidawa Kotu
Ba zan iya aiki ba tare da zuƙar Tabar Wiwi ba - Wani Mutum ya shaidawa Kotu

Yake cewa, a sanadiyar yanayin aikin sa na haƙar ramuka da kuma yasa rijiya da masai, ya sanya a wani sa'ilin yake zuƙar tabar sa domin ya ji dadin aiki.

KARANTA KUMA: An gudanar da 'Kidayar adadin Awakai a 'Kasar Zambia

Mukundi a yayin amsa laifin sa na mallakar tabar wiwi, ya kuma yi ƙorafi a gaban kotun da cewa, jami'an 'yan sandan yayin cafke sa sun ci zarafin sa da har ta kai ga sun raunata shi.

A sanadiyar haka Kotun ta bayar da umarni ga jami'an 'yan sanda akan su gabatar da cikakken bayani dangane da cafke wannan matashi domin tabbatar da gaskiyar ƙorafin sa.

Legit.ng ta fahimci cewa, kotun ta bayar da belin Mukundi inda kuma ta daga sauraron karar sa zuwa ranar 30 ga watan Agusta na 2018.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel