An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji

An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji

Hukumar yaki da fasa kauri, wanda aka fi sani da suna Kwastam ta cafke wani babban sunduki da aka shigo dashi Najeriya makare da kayan sawan Sojoji da dama, inji rahoton jaridar Punch.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito mataimakin shugaban kwastam na yankin Fatakwal, Sanusi Umar ne ya sanar da haka a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta, inda yace kayan sun hada da wando da rigan Kaki guda 620, kanaan riguna yan ciki na Soja guda 10,100 sai kuma takalman Sojoji kafa 512.

KU KARANTA: Mai martaba Sarkin Daura ya nada Orji Uzor Kalu wata babbar sarauta a masarautar Daura

Kwantrola Sanusi yace: “A yau mun kama wani sunduki mai lamba MRKU 4909151 dake cike makil da kayan sawan Sojoji, mallakin kamfani Ehiogocho Nigeria Limited, kamfanin da muka kama ta da shigo da sunduki cike da kayan Sojoji mako biyu da suka gabata, mai kamfanin shine Ongwatabo Jerry.

An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji
Kakin Sojoji

“Bincikenmu ya nuna akwai kayan Sojoji a cikin sundukin da suka hada da wando da rigan Kaki guda 620, kanaan riguna yan ciki na Soja guda 10,100 sai kuma takalman Sojoji kafa 512, wanda hakan haramun ne a Najeriya bisa dokokin hukumar Kwastam.” Inji shi.

An sake kwatawa: Kwastam ta kama wani babban sunduki da ya shigo Najeriya makare da kakin Sojoji
Kakin Sojoji

Daga karshe anyi canjin shugabanci, inda kwantrola Abubakar Bashir ya mika ragamar mulki ga sabon kwantrola Saidu Galadima, inda Galadima ya ja hankalin jami’an kwastam dake yankin dasu guji cin hanci da rashawa, kuma su yi aiki da kishin kasa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel