Da kayu: Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda, hotuna

Da kayu: Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda, hotuna

A yau ne hukumar ‘yan sanda a jihar Kano, ta bakin kakakinta, SP Magaji Musa Majiya, ta sanar da yin bajakolin wani babban ta’adda, Rabi’u Suleiman, dan asalin kauyen Fadar Yalwa dake karkashin karamar hukumar Tudun Wada, da ke kera bindigu kala daban-daban yana sayar wa da masu aikata miyagun laifuka.

Majiya ya bayyana cewar Rabi’u na sayar da bindigun da yake kerawa ga ‘yan fashi da suka addabi jama’a a dajin Falgore da kuma masu fashi a kan babban titin Kano zuwa Zaria da ragowar wasu sassan jihar Kano.

An kama Rabi’u da bindigu kala-kala da alburusai masu yawa kamar yadda ku ka gani a hotunan dake cikin wannan labara. Ana cigaba da gudanar da bincike a kansa kafin a gurfanar das hi gaban kotu.

Da kayu: Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda, hotuna
Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda

Da kayu: Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda, hotuna
Hukumar ‘yan sanda a Kano ta kama kasurgumin dan ta’adda

A wani labarin na nij.com kun ji cewar wata babbar kotu dake zamanta a Ilorin, babban birnin jihar Kwara, karkashin mai shari’a, Ibrahim Yusuf, tayi barazanar tisa keyar babban sifetan hukumar ,yan sandan Najeriya, Idris Ibrahim, zuwa gidan yari saboda raina umarninta.

DUBA WANNAN: Gwamnonin Najeriya sun fara kwalo-kwalo a kan batun karin albashi

Kotun na zargin Idris da raina umarninta na sakin Mista Olalekan Alabi, wani mataimaki na musamman a kan harkokin siyasa ga gwamnan jihar Kwara, Abdulfatah Ahmed.

Barazanbar tura Sufeto Idris gidan yarin na kunshe ne cikin wata takardar jan kunne mai lamba ta 48 da kotun ta buga a ranar 10 ga watan Agusta. Takardar da aka raba ga manema labarai yau, Alhamis, a Ilorin ga manema labarai na dauke da saka hannun rajistaran kotun.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Khadijah Thabit avatar

Khadijah Thabit (Copyeditor) Khadijah Thabit is an editor with over 3 years of experience editing and managing contents such as articles, blogs, newsletters and social leads. She has a BA in English and Literary Studies from the University of Ibadan, Nigeria. Khadijah joined Legit.ng in September 2020 as a copyeditor and proofreader for the Human Interest, Current Affairs, Business, Sports and PR desks. As a grammar police, she develops her skills by reading novels and dictionaries. Email: khadeeejathabit@gmail.com