Babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu

Babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu

Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun Talata, 21 ga watan Agusta, da Laraba, 22 ga watan Agusta a matsayin ranakun hutu domin murnar babbar salla (Eid-el-Kabir).

Ministan harkokin ciki gida, Abdulrahman Dambazau, ne ya sanar da hakan yau, Alhamis, a Abuja a wata sanarwa da Umar Mohammed, babban sakataren ma’aikatar ya sakawa hannu.

Babbar Sallah: Gwamnatin tarayya ta bayyana ranakun hutu
Dambazau

Gwamnatin tarayya ta taya ‘yan Najeriya murnar zagayowar babbar sallar tare da yi masu fatan yin bukukwan sallah lafiya.

Kazalika, gwamnatin ta bukaci ‘yan Najeriya su rungumi soyayya da kaunar juna domin samun zamana lafiya mai dorewa, kamar yadda Dambazau ya sanar.

DUBA WANNAN: Kotu ta yiwa babban sifeton 'yan sanda albishir da tura shi gidan yari

Dambazau ya bukaci ‘yan Najeriya dake gida da kasashen ketare das u cigaba da bawa gwamnatin shugaba Buhari hadin kai musamman a kokarinta na tabbatar da zaman lafiya da hadin kai a tsakani jama’a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng