Na yafewa duk wadanda suka gana min azaba ta tsawon shekara 15 – Al-Mustapha
Manjo Hamza Al-Mustapha, tsohon dogarin tsohon shugabn kasar Najeriya a mulkin soji, marigay Janar Sani Abacha, ya bayyana cewar ya yafewa dukkan masu hannu cikin ukubar da aka shafe shekara 15 ana gana masa.
An kama tare da tsare Al-Mustapha ne bisa zarginsa da kisan Kudirat Abiola, uwargidan mutumin da ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993, marigayi Moshood Abiola.
Da yake jawabi a wani taro na kungiyoyin Kiristoci fiye da 40, Al-Mustapha, ya bayyana cewar ya yafewa kafatanin masu hannu a daurin da aka yi masa.
DUBA WANNAN: Mata biyar da suka fi shahara a duniya
A cewar Al-Mustapha, sau 11 ana yunkurin hallaka shi a kan laifin da bai san komai a kai ba amma Allah yana kubutar da shi.
Sannan ya kara da cewar akwai wasu muhimman bayanai da ya samu a kan kungiyar Boko Haram lokacin da yake gidan yari tare da bayyana cewar wasu ‘yan boko ne suka kirkiri kungiyar.
“Sun kawo ‘yan Boko Haram 138 dakin da nake a gidan yari, bayanan da suka sanar da ni ba zan iya fadawa ‘yan Najeriya ba saboda dalilan tsaro” a cewar Al-Mustapha.
Kazalika ya bayyana cewar an kirkiri rikicin makiyaya da manoma dagan-gan domin kawar da hankalin ‘yan Najeriya daga wasu abubuwa dake faruwa a kasa. Sai dai bai bayyana ko wadanne abubuwa ne ba.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng