Farin jini: Masu shaguna a Saudiyya na amfani da hoto da sunan Buhari domin samun kasuwa

Farin jini: Masu shaguna a Saudiyya na amfani da hoto da sunan Buhari domin samun kasuwa

Wasu ‘yan kasuwa a kasar Saudiyya na fuskantar rashin ciniki saboda banbancin yare dake tsakaninsu da bakin mahajjata.

Sai dai wasu ko kadan basa fuskantar wannan matsala saboda su kan iya yin Magana da yaren Hausa da kuma na Turanci musamman domin jan hankalin mahajjata daga Najeriya.

Bugu da kari wasu daga cikin ‘yan kasuwar na kasar Saudiyya sun fahimci abinda baki daga Najeriya ke kauna tare da girmamawa kuma suna amfani da wannan dammar domin samun kasuwa.

Wasu mahajjata sun tabbatar da cewar wasu shagunan sayar da kaya a Madinah na kwalla ihun “sai Buhari” domin jawo hankalin ‘yan Najeriya su shiga shagon su yi sayayya.

Farin jini: Masu shaguna a Saudiyya na amfani da hoto da sunan Buhari domin samun kasuwa

Wani mai shago a Saudiyya

Kalmar “sai Buhari” ko “sai Baba” ta zama gama-gari a tsakanin ‘yan Najeriya, musamman ‘yan arewa, tun bayan shigowar Buhari siyasa a shekarar 2002.

Yanzu haka ‘yan kasuwa Larabawa a kasar Saudiyya sun ari wannan kalma domin neman kasuwa da bunkasa cinikayya tsakaninsu da mahajjata daga Najeriya.

DUBA WANNAN: Saraki zai yi takara da Buhari a 2019

Tawagar alhazan Najeriya daga jihar Kaduna sun tattauna da wasu da wasu daga cikin ‘yan kasuwar kasar ta Saudiyya a birnin Madina domin sanin dalilinsu na yin amfani da Kalmar “sai Baba” domin jawo hankalin kwastomas.

Muhammad da Afnan ‘yan kasar Bengaladash ne dake da shagon sayar da dogwayen riguna(jallabiya) a Madina kuma sun bayyana cewar suna amfani da sunan Buhari ne don kiran kwastomas bayan sun fahimci cewar ‘yan Najeriya na matukar kauna da girmama shugaba Buhari.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel