Zamu maka Najeriya a duhu - Ma'aikatan lantarki sun yi barazanar yajin aiki

Zamu maka Najeriya a duhu - Ma'aikatan lantarki sun yi barazanar yajin aiki

Ma'aikatan wutan lantarki na kasa sun bukaci a tsige, Usman Muhammed, shugaban kamfanin rabar da lantarki na kasa (TCN).

Ma'aikatan ta suka shigar da korafin sun karkashin kungiyar ma'aikatan wutan lantarki da kamfanonin wuta (SSAEAC) suna zargin Muhammad da babakere da aikata wasu ayyukan da suka sabawa dokikin kungiyar kwadago.

Sunyi wannan korafin ne jiya Talata a Abuja, inda su kayi barazanar shiga yajin aiki da zai katse samar da lantarki a kasar baki daya idan ba'a biya musu bukatunsu ba.

Ma'aikatan wutan lantarki na kasa sunyi barazanar zuwa yajin aiki
Ma'aikatan wutan lantarki na kasa sunyi barazanar zuwa yajin aiki

Umar Abubakar, Sakatare Janar na SSAEAC, ya ce Muhammad ya saba dokokin aiki a hukumar wanda hakan ya tauye wa ma'aikata hakokinsu da hana su samun walwala.

DUBA WANNAN: Lalata don bayar da maki: An sake fatatakar wani lakcara a wata jami'ar Najeriya

Har ila yau, ma'aikatan suna zargin shugaban na TCN da tsara jarabawar karin girma na ma'aikata shi kadai ba tare da tuntubar sauran ma'aikatan kamfanin ba.

Kazalika, sun kuma yi ikirarin cewa Usman Muhammad baya biyan cikaken haraji ga hukumar tara haraji na kasa (FIRS).

A cikin wasikar da ma'aikatan suka rubuta don bayyana rashin jin dadinsu, sun zargi Muhammad da karkatar da kudaden tallafi da Bankin Duniya ta baiwa kamfanin saboda inganta samar da wutan lantarki a kasa.

"Niyyarsa shine kin yin karin girma ga ma'aikata musamman wadanda suka cancanta ayi musu karin girmar saboda kwarewa da kwazonsu.

"Muna zargin yana son ya dauki ma'aikata ne wadanda zasu rika yi masa biyaya ko da yana saba doka." inji mai'aikatan.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164