Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

Wato jigo a tafiyar Kwankwasiya a jihar Kano, Hajiya Binta Spikin, tayi tsokaci kan batun zuwan Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jihar Kano bayan sauya shekarsa zuwa jam'iyyar adawa ta PDP inda tace Kwankwaso zai ziyarci Kano idan lokaci ya yi.

Binta Spikin ta shaidawa Vanguard cewa, "Tabbas Sanata Rabiu Musa Kwankwaso zai kawo ziyara Kano kuma idan lokacin ya yi, babu mahalukin da ya isa ya hana shi zuwa."

Hajiya Binta kuma ta bayyana gamasuwarta kan yadda magoya bayan Kwankwaso suke cigaba da bashi goyon baya kuma ta kara da cewa "zamu cigaba da gwagwarmaya don tabbatar da cewa PDP ta amshe mulki a Kano da ma Najeriya baki daya."

Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

Bayan kai ruwa rana a baya, yanzu Kwankwaso zai ziyarci Kano

DUBA WANNAN: Mata biyar da suka fi shahara a duniya

Wata jagoran mata a Kwankwasiya, Hajiya Atine Abdullahi itama tayi karin haske kan batun ziyarar inda tace Kano ta Kwankwaso ne kuma Kwankwaso na Kano ne.

Kalamanta: "Sanata Kwankwaso dan Kano ne kuma Kano tasa ce shima na Kano ne.

"Kwankwaso cikaken dan asalin jihar Kano ne. Babu wanda ya isa ya hana shi shiga garin Kano."

Sanata Kwankwaso yana daya daga cikin manyan masu adawa da gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Ganduje, wanda shine mataimakin Kwankwaso lokacin da yake gwamna a jihar Kano.

A watan Janairun wannan shekarar, Hukumar 'yan sandan Najeriya ta shawarci Kwankwaso ya dage ziyarar da ya yi niyyar kaiwa jihar Kano har sai takkadamar dake tsakanin magoya bayansa da na gwamna Ganduje ta lafa duk da cewa a lokacin suna jam'iyya daya.

Tun wannan lokacin, Sanata Kwankwaso bai ziyarci jihar Kano ba hakan kuma ya jefa jama'ar mazabarsa cikin damuwa da fargaba.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel