Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

A ‘yan shekarun bayan-bayan nan an samu yawaitar jaruman masana’antar shirya fina-finai ta kudu da aka kira Nollywood da suka bar addinin iyayensu tare da rungumar addinin Musulunci.

Jaridar Legit.ng ta tattara 6 daga cikin irin wadannan jarumai domin kawowa masu karantu dan takaitaccen tarihin su.

1. Mawakiya Moji Olaiya: Moji ta kasance mawakiya a masana’antar Nollywood wacce ta tashi a matsayin Kirista duk da kasancewar mahaifiyar ta Musulma.

Moji ta Musulunta ne bayan ta sha fama da matsalar aure tsakaninta da mazaje biyu da ta aura.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Mojo Olaiya

Yayin wata da aka yi da ita, Moji ta bayyana cewar “addininin musulunci addini ne mai sauki. Matukar kai musulmi ne to daya kake da dukkan musulmi kuma babu bukatar sai wani ya yi maka iso wurin Allah ko ya nema maka wani abu wurinsa. Shine abinda ya fi birgeni da addinin.”

2. Vivian Metchie: Haifaffiyar kirista ce ta kowanne bangare, Vivian ta girma cikin addinin kiristanci kuma ta auri miji Kirista har sun haifi ‘ya’ya hudu.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Vivian Metchie

Ta bayyana cewar rudanin da ta shiga a kan addinin kirista, musamman rabuwar kayuwa ya saka ta shiga Musulunci, addinin da ta ce ta samu kwanciyar hankali a cikinsa.

3. Liz Da Silva: Ita ma kamar Vivian, an haifeta ne cikin addinin Kirista har zuwa aurenta na farko da Musliu Akinsanyawanda.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Liz Da Silva

Bayan rabuwar aurensu ne ta auri wani Musulmi mai suna Olaoye wanda bayan sun haihu tare da shi sai ta musulunta har ma ta canja sunanta zuwa Aisha.

4. Laide Bakare: Kyakykyawar jaruma, Laid eta musulunta bayan aurenta na farko da mijinta Kirista ya mutu kuma ta auri Musulmi, hamshakin mai kudi a Legas, Alhaji Tunde Orilowon.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Laide Bakare

5. Lola Alao: Lola ba ta dade da barin addinin Kirista ba. Fitar daga Kiristanci ta jawo cece-kuce a dandalin sada zumunta musamman Facebook.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Lola Alao

6. Lizzy Anjorin: Asalin sunanta shine Elizabeth Anjorin amma daga baya ta canja bayan ta shiga masana’antar Nollywood.

Lizzy ta bayyana cewar tun farko tana da alaka mai kyau tsakaninta da Musulunci domin mahaifiyarta Musulma ce.

Suna da hoto: Fitattun jaruman Fim din kudu 6 da suka musulunta

Lizzy Anjorin

Wasu na alakanta batun musuluntar tad a kusancin da take das hi da wannan babban Alhaji a Legas.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel